Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Joe Biden: Ina ganin George Floyd zai kawo sauyi a duniya
Dan takarar shugabancin Amurka na Jam'iyyar Democrat Joe Biden ya ce marigayi George Floyd zai kawo "sauyi a duniya."
Bayan tattaunawar sirrin da ya yi da iyalan Mr Floyd a Houston, Texas, domin mika ta'aziyyarsa game da rasuwarsa, Mr Biden ya shaida wa gidan talbjin na CBS cewa mutuwar Floyd tana "daya daga cikin manyan abubuwan da za su kawo sauyi a tarihin Amurka".
Kisan da 'yan sandan Amurka suka yi wa bakar fata George Floyd ya haddasa zanga-zanga a fadin duniya.
Nan gaba kadan a yau ne za a yi jana'izarsa a Houston.
"Iyalansa mutanen kirki ne, 'yarsa tana wurin kuma ta ce 'mahaifina zai sauya duniya,' kuma ni ma ina ganin mahaifinta zai kawo sauyi a duniya," Mr Biden ya shaida wa mai shirin na CBS Norah O'Donnell.
"Ina ganin abin da ya faru a nan shi ne daya daga cikin manyan batutuwan da suka faru a tarihin Amurka, tabbas, a game da 'yancin dan adam da kuma yadda ake mutunta shi ko akasin hakan."
Mai magana da yawun iyalan Floyd Benjamin Crump, wanda ya wallafa hoton ganawar, ya ce iyalan Mr Floyd sun yi maraba da kalaman Mr Biden.
Ya kara da cewa "Tausayawar da ya yi wa iyalansa ta burge su."
Masu taimaka wa tsohon mataimakin shugaban kasar sun ce zai fitar da sakon bidiyo wanda za a gabatar a yayin jana'izar Mr Floyd ranar Talata.
Masu halartar jana'iza a Houston, da ke Texas, inda Mr Floyd ya zauna kafin ya koma Minneapolis, sun tsaya kan wani dogon layi domin kallon gawarsa, wacce aka ajiye a bainar jama'a tsawon awa shida domin mutane su yi mata bankwana a cocin The Fountain of Praise.
Tuni aka gudanar da addu'o'i a Minneapolis da North Carolina, inda aka haifi Mr Floyd.
Sababbin bayanai kanmutuwar George Floyd
Derek Chauvin, tsohon dan sandan Minneapolis wanda aka zarga da kisan Mr Floyd ya bayyana a karon farko a gabana kuliya raar Litinin, inda aka bayar da belinsa a kan $1.25m.
Chauvin - wanda ya sanya gwiwarsa ya danne wuyan Mr Floyd tsawon minti takwas - yana fuskantar zargin kisan kai. Ana zargin 'yan sanda uku da laifin taimakawa wajen yin kisan kai.
Masu shigar da kara sun bayyana "girman laifukan" da kuma tunzura jama'ar da kisan ya yi a matsayin dalilan da suka sanya aka kara kudin bayar da belin zuwa $1m.
Zai sake gurfana a kotu ranar 29 ga watan Yuni.
A gefe guda, Majalisar wakilan Amurka wadda 'yan jam'iyyar Democrat ke da rinjaye a cikinta ta fitar da wani daftarin doka da za ta yi wa ayyukan 'yan sanda garambawul.
Daftarin zai ba masu shigar da kara saukin tuhumar 'yan sandan da suka aikata laifukan take hakkin jama'an da ya kamata su ba kariya, kuma za ta haramta wasu dabi'u da 'yan sanda ke amfani da su kan mutane kamar shakewa da makarewa, ta kuma duba batun nuna bambancin launin fata.
A ranar Litinin, majalisar birnin Minneapolis - birnin da aka kashe George Floyd - ta kada kuri'ar rusa rundunar 'yan sandan birnin tare da yin garambawul ga dukkan ayyukan 'yan sanda.
Zanga-zangar kyamar wariyar launin fata baya kisan Mr Floyd ta shiga mako na uku a Amurka. An gudanar da manyan gangami a birane da dama, cikinsu har da Washington DC, New York, Chicago, Los Angeles da kuma San Francisco.