Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Aisha Buhari: 'Matsalar fyade na tayar mini da hankali'
Aisha Buhari, mai dakin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ta ce labarin da take samu game da yawaitar yi wa mata fyade yana matukar tayar mata da hankali.
A sakon da ta wallafa ranar Laraba a shafinta na Twitter, Aisha Buhari ta ce: "Abin tayar da hankali ne samun labarin kisan da ake yi wa 'ya'yanmu mata, wadanda maza suke yi wa fyade na rashin imani; wasu lokutan ma iyayensu da 'yan uwansu da kuma masu kula da su ne suke yin hakan."
Matsalar fyade dai tana neman zama ruwan dare a Najeriya, inda a baya bayan nan aka samun labarin yi wa wasu mata fyade a sassa daban-daban na kasar.
Daya daga cikinsu ita ce wata yarinya mai shekara 12 wacce ta shaida wa 'yan sanda a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin kasar cewa wasu mutum 12 sun shafe wata biyu suna yi mata fyade.
Kazalika, a makon jiya an zargi wasu mutane da kisan wata ɗaliba ƴar jami'a bayan sun yi mata fyade a jihar Edo da ke kudancin Najeriya.
Masu rajin kare hakkin yara a Najeriya na ganin cewa za a ci gaba da fuskantar matsalar fyade ga kananan yara a kasar matukar gwamnati ba ta fara aiwatar da hukuncin kisa a kan masu aikata irin wannan laifi ba.