Romina Ashrafi: 'Yan sanda sun kama mutumin da ya kashe 'yarsa a Iran

An yi zargin cewa mahaifin Romina Ashrafi ya far mata tana tsaka da bacci

Asalin hoton, Twitter

Bayanan hoto, An yi zargin cewa mahaifin Romina Ashrafi ya far mata tana tsaka da bacci

'Yan sanda a arewacin Iran sun kama wani mutum da ake zargi da kashe 'yarsa mai shekara 14 "domin ya kare mutuncin danginsa" lamarin da ya jawo Allah-wadai a kasar.

Romina Ashrafi ta tsere daga gidansu da ke lardin Gilan tare da saurayinta mai shekara 35 bayan mahafinta ya ki amincewa ta aure shi, a cewar kafafen watsa labaran kasar.

'Yan sanda sun gano masoyan biyu inda suka aika Romina gida duk da rahotannin da ke cewa tana fargabar barazana ga rayuwarta.

A daren Alhamis din da ta gabata, an yi zargin cewa mahaifinta ya far mata tana tsaka da bacci.

Kafar watsa labarai ta Gilkhabar.ir ta rawaito cewa an "gididdiba" Romina da lauje kuma bayan haka ne mahaifinta ya fice daga gidan "da laujen a hannunsa inda ya yi ikirarin kashe ta".

Ranar Laraba, jaridun kasar da dama sun wallafa labarin kashe Romina a matsayin babban labarinsu.

Masu amfani da Twitter sun kirkiro mau'udin #Romina_Ashrafi don yin tur da kisan ta kuma an yi amfani da shi fiye da sau 50,000.

Shahindokht Molaverdi, tsohuwar mataimakiyar shugabar harkokin mata da iyali kuma sakatare ta Kungiyar kare hakkin mata ta Iran, ta rabuta cewa: "Romina ba ita ce mace ta farko ba kuma ba za ta zama mace ta karshe ba da aka kashe don "kare martabar iyali".

Ta kara da cewa za a ci gaba da aiwatar da irin wadannan kashe-kashe "matukar ba a yi watsi da al'adu da dabi'un da basu dace ba".