Mutum 65 ne suka kamu da cutar korona a Kano ranar Lahadi

Asalin hoton, SALIHU TANKO YAKASAI FACEBOOK
Hukumomi sun tabbatar da gano mutum 65 da cutar korona ta kama ranar Lahadi, kwana guda bayan gano mutum uku da suka harbu.
Yawan mutanen da cutar ta shafa zuwa daren ranar ya kai 1,520 cewar ma'aikatar lafiya ta jihar Kano.
Alƙaluman ma'aikatar sun kuma nuna cewa yanzu haka mutum 262 ne ke kwance suna ci gaba da jinya a cibiyoyin kula da masu korona da ke jihar.
Yanzu dai Jihar ta koma mataki na shidda sabanin ta bakwai da take a baya, bayan da ta zarce jihar Delta.

Asalin hoton, Reuters

Ma'aikatar lafiya ta jihar Kano ta ce a ranar Lahadi an sallami mutum 15 da suka warke daga cutar, domin su koma gida cikin iyalansu.
Hakan na nufin Jihar na bayan jihohi biyar, da suka hadar da Legas mai mutum 14,456, da Abuja mai mutum 3,481, da kuma Oyo mai 2,575, da Edo mai mutum 2,116 da kuma jihar Rivers mai mutum 1,652,.
Adadin na ƙaruwa ne duk da matakan da gwamnatin tarayya da na jihohi ke dauka wajen dakile cutar.
A Najeriya baki daya an ƙara gano mutum 555 da suka kamu da korona ranar Lahadi.











