Coronavirus: Yaya Sallar Eid ta bana ta zo muku?

    • Marubuci, Ishaq Khalid
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja

Yayin da azumin watan Ramadan ya kawo karshe, al'ummar Musulmi a sassa daban-daban na duniya na gudanar da shagulgulan karamar Sallah.

A kasashe da dama dai an dakatar da tarukan ibada saboda cutar korona.

Bukukuwan karamar Sallah na cikin manyan sunnoni a addinin Islama bayan kammala azumin Ramadan. To ko yaya sallar bana ta zo wa Musulmi a Najeriya?

Wasu magidanta babu halin sayen kayan Sallah

Kamar yadda azumin watan Ramadan na bana ya zo, ita karamar Sallah haka ta zo wa Musulmi a wani yanayin da galibin jama'a ba su taba ganin irinsa ba a rayuwarsu

Dalili kuwa shi ne annobar cutar korona wadda ta janyo takaita zirga-zirga da hana tarukan ibada.

Musulmi na bayyana yadda suke tunkarar karamar sallar. Malam Musa Mesin, wani magidanci a Abuja, ya shaida mini cewa yanzu dai ya zuba wa sarautar Allah ido.

Domin ba shi da kudin abinci, babu na kayan sallah, ga shi kuma hukumomi a birnin sun hana zuwa masallacin idi domin hana yaduwar cutar.

Malam Musa, wanda magini ne, ya ce sakamakon zuwan cutar korona, harkoki sun tsaya cak kuma "duk mai karamin karfi da ke Najeriya, ya shiga halin ha'ula'i."

"Batun kayan sallah na yara, ko nawa, gaskiya babu. Kuma babu halin saya. Amma watakila idan Allah Ya kawo sai a yi. Da kamar wuya dai domin sallar ta riga ta zo," in ji shi.

Sai dai ya yi fatan za a yi Sallah lafiya, yana mai cewa ko da yake bai ji dadin yadda ba za a yi tarukan Sallah a Abuja ba, amma a shirye yake ya yi wa hukumomi biyayya kan wannan umarni.

Da ma tun kafin bullar cutar korona, Najeriya na cikin kasashe da jama'arsu suka fi fama da talauci, kuma masana da hukumomi na gargadin cewa tattalin arzikin kasar zai daɗa shiga wani mawuyacin hali.

Wannan kuma zai iya kara jefa jama'a cikin talauci.

Yaya batun kajin Sallah?

Duk da cewa cutar korona ta takaita manyan hidimomi, kuma jama'a da dama na fama da rashin kudi, to amma wasu musulmin na ƙuƙutawa suna tanadar kayayyaki domin bikin Sallah.

A wata kasuwar kaji da ke unguwar Gwarinpa cikin birnin Abuja, na ga kaji da dama amma masu saya kalilan. Wasu kajin a cikin keji, wasu a kasa a daure, yayin da wasu kuma ana sauke su daga mota.

Mutane dai na ɗan zuwa suna sayen kaji. Sai dai 'yan kasuwa na cewa ba kamar yadda aka saba ba.

Daya daga cikin masu sayarwa da kuma gyara kajin, Anas Saidu, ya ce a Sallar bara, sukan yanka kaza 10 zuwa 60 a lokaci guda, amma yanzu sukan yanka kaza biyu zuwa 10 ne kacal.

Ya ce: "Saboda da halin da aka shiga na cutar koronabairus, yanayin kasuwa sai a hankali".

A galibin jihohin arewacin Najeriya, ciki har da mafi yawan jama'a wato Kano, hukumomi sun janye dokar hana tarukan ibada, wasu kuma da ma ba su kafa dokar ba, matakin da ya ba da damar yin Sallar Juma'a da kuma ta Idi.

Amma a wurare kamar jihohin Kaduna da Filato da kuma Abuja babban birnin Najeriya, bisa dukkan alamu ba za a gudanar da tarukan sallar Idin ba domin ba a sassauta dokar hana tarukan ibada ba - kuma wannan shi ne karon farko da musulmi da dama ke ganin irin wannan yanayi.

Hasali ma shi kansa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce shi da iyalansa za su yi tasu Sallar Idin a gida domin yin biyayya ga dokar hana fita da aka sanya a Abuja da kuma umarnin Sarkin Musulmi na cewa kowa ya yi sallar Idi a gida.