Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Ko an bi tsarin tazara wajen sallar Juma'a a Kano?
Dubban mutane ne suka halarci sallar Juma'a a birnin Kano da kewaye, ranar farko kenan da aka buɗe masallatai bayan kusan mako biyar sakamakon annobar korona.
Masallacin Umar Ibn Khattab da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso a birnin Kano na ɗaya daga cikin masallatan da jama'a suka yi wa tsinke.
Wakilin BBC Mansur Abubakar ya ce kasancewar wannan ce Juma'a ta ƙarshe a watan Ramadana, hakan ya ƙara jawo cikar jama'a a masallatan.
Wasu da suka halarci sallar sun shaida wa BBC cewa tun karfe 9:00 na safe suka je masallaci saboda tsananin murna ganin cewa an kwana biyu ba a yi Juma'a ba a jihar.
Wakilin namu ya bayyana cewa masallatai da dama sun yi ƙoƙari wajen bin ƙa'idojin da gwamnati ta gindaya ta hanyar ajiye ruwan wanke hannu da sauransu.
Kazalika ya tarar da 'yan agaji a ƙofar masallacin, inda akasarin waɗanda ke sanye da takunkumi suke cikin masallaci.
Sai dai kuma wasu ba su saka takunkumin ba, inda akasarinsu suka zauna a wajen masallaci.
Wasu da ke ciki da wajen masallacin kuma ba su ba da tazara yadda ya kamata ba kamar yadda gwamnati ta bayar da umarni.
An shafe kusan mako biyar ba a gudanar da sallar Juma'a ba a Kano sakamakon dokar da aka saka ta hana taron mutane a yunƙurin daƙile cutar korona.
Sai dai a wannan makon, gwamnatin jihar ta Kano ta gindaya wasu sharuɗɗan da za a bi domin gudanar da sallolin Juma'a da Idi da ta amince za a yi.