Coronavirus: Saudiyya ta mayar da 'yan Najeriya kusan 300 gida

Sarki Salman

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama ya ce sun karbi 'yan Najeriya mutum 292 da suka makale a Saudiyya.

Ministan wanda ya wallafa bayanin a shafinsa na Twitter ya ce jirgin Saudiyya ne ya kai mutanen filin jirgin sama da ke birnin Abuja a daren Talata.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Ya kara da cewa mafi yawancin mutanen da aka mayar da su Najeriyar mata ne masu shayarwa da kananan yara.

Sai dai ya ce yanzu haka an killace su a otal har zuwa makonni biyu kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanadar wajen gane ko suna dauke da cutar korona ko a a.

Wannan ce dai tawaga ta baya-bayan ta 'yan Najeriyar da suka makale a kasashen waje a zamanin korona.

Kusan dai wannan ne karon faro da wata kasa ta mayar da 'yan Najeriya ga kasarsu sakamakon annobar korona da ta katse wa matafiya da dama hanzari.

A baya dai Najeriya ta yi jigilar 'yan kasar tata daga Burtaniya da Amurka da Hadaddiyar Daular Larabawa.