Coronavirus a Kano: Ƙarin mutum 2 sun mutu, masu warkewa sun ƙaru

Gwamna Abdullahi Ganduje

Asalin hoton, KNSG

Lokacin karatu: Minti 2

Ma'ikatar lafiya ta Kano da ke arewacin Najeriya ta ce ba a samu wanda ya harbu da cutar korona ba ranar Asabar a jihar, sai dai cikin masu dauke da cutar 2 sun mutu.

Alkaluman da ma'aikatar ke fitarwa na nuna cewa ana samu ragin yaduwar cutar inda a yau Asabar babu ko mutum daya da gwaji ya nuna na dauke da cutar.

Jihar Kano dai ta fi fama da annobar a arewacin Najeriya, da yawan masu cutar 761.

Haka kuma an samu karin mutum uku da suka warke kuma aka sallame su daga asibiti sakamakon korona a Kano. Yanzu adadin mutanen da suka warke a Kano sun kai 93 a daren Asabar.

Adadin mamata sakamakon wannan cuta yanzu ya kai 35.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

BBC
Karin bayani kan coronavirus

Jadawalin jiha 34 da birnin Abuja da cutar ta bulla ya nuna Kano ce har yanzu ta biyu a yawan masu cutar korona da mutum 761, a bayan Legas mai mutum 2,373.

Gwamnatin Kano dai ta tsawaita dokar kulle da mako guda a kokarinta na shawo kan annobar, ko da yake malaman addini a jihar na ta da a sassauta dokar musamman don ba da zarafin halartar masallatan Juma'a.

Jihohi kamar Jigawa da Borno sun sanar da dage dokar inda suka bai mutane damar halartar sallolin jam'i, musamman na Juma'a da na sallar idi mai zuwa.

Alkaluman da hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Najeriya ta fitar a daren Asabar sun nuna cewa yawan masu korona a Katsina sun kai 239, Jigawa na da mutum 197, sai Kaduna mai 138.

Ya zuwa daren Asabar 16 ga watan Mayu, mutum 5,621 ne suka harbu da korona a daukacin Najeriya, cikinsu, 176 sun rasu sakamakon cutar yayin da 1,472 suka warke kuma aka sallame su.