An dawo Bundesliga amma ba ƴan kallo

Bundesliga ta Jamus

Asalin hoton, Getty Images

An dawo da buga wasannin gasar Bundesliga ta Jamus a ƙarshen makon nan bayan dakatar da wasannin saboda cutar korona.

Za a buga wasannin ne amma ba tare da ƴan kallo ba, saboda tsoron ƙara yaduwar cutar korona.

Wasanni shida za a buga a ranar Asabar, karon farko tun dakatar da wasannin gasar a ranar 13 ga Maris waɗanda suka haɗa da wasan hamayya tsakanin Borussia Dortmund da Schalke.

Kuma yanzu duka lokaci ɗaya za a buga wasannin tsakanin Borussia Dortmund da Schalke, sai wasa tsakanin Augsburg da Wolfsburg, Düsseldorf da Paderborn.

RB Leipzig da Freiburg. Hoffenheim da Hertha Berlin. Daga baya kuma Frankfurt za ta kara da Borussia Mgladbach

Za a girke jami'an tsaro a filayen wasannin domin tabbatar da magoya bayan ƙungiyoyin ba su shiga ba ko yin kutse domin kallon wasannin ba, yayin da ake fargaba kan masu zanga-zangar adawa da dokar kulle.

An ɗauki tsauraran matakai na hana wa ƴan kallo shiga filayen wasannin.

Kimanin mutane 300 ne kawai za su kasance a fili, da suka haɗa da ƴan wasa da kuma masu horar da su.

Sai da aka yi wa ƴan wasa gwajin cutar korona kafin dawo da wasannin. Kuma ana tunanin za a kiyaye bada tazara tsakanin jami'ai da sauran 'yan wasa da ke gefe fili.

Sai da aka killace dukkanin tawagar ko wace ƙungiya, a otel otel zuwa filin da suke atisaye na tsawon mako ɗaya kafin a dawo buga wasannin.

Bayern Munich ce saman teburin Bundesliga da maki 55, tazarar maki hudu tsakaninta da Borussia Dortmund.