Gwamnati za ta bude kofa ga gasar firimiyar Ingila

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Burtaniya ta ce za ta bude kofa don ganin yadda za a koma harkokin kwallon kafa na kwararru a Ingila cikin watan Yuni.
Bayan wata ganawa da hukumomin kwallon kafa, sakataren al'adu Oliver Dowden ya ce an samu ci gaba kuma suna duba yiwuwar samun karin kafar da masu sha'awar kwallo za su kalle shi kai tsaye a talabijin.
Sai dai wani babban jami'in lafiya a Ingila y ace za su bi abin sannu-sannu.
Ranar 13 ga watan Maris ne aka jingine gasar firimiyar Ingila, kuma akasarin kulob-kulob na da sauran wasa tara a gabansu.
Kungiyoyin gasar firimiyar Ingila sun gana a ranar Litinin da ta wuce inda suke sa ran soma kwallon kafa a ranar 12 ga watan Yuni amma ba tare da 'yan kallo ba.







