Coronavirus: Me ya sa Gwamna Wike ya ruguje otal guda biyu?

Nyesom Wike

Asalin hoton, Twitter

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom WIke ya ce masu otal-otal din sun yi wa dokar hana zirga-zirga karan tsaye.

Batun rushe otal guda biyu da gwamna Wike na Rivers ya yi a karamar hukumar Eleme na ci gaba da bai wa jama'a al'ajabi.

An dai ce wasu mutane ne ke yin sharholiya a wani otal mai suna Prodest ain da ya sa wani ya kai tseguminsu ga kwmaitin gwamnatin jiha mai yaki da cutar korona, inda kwamitin ya je otal din.

Ana cikin hakan ne sai wani matashi dan jam'iyyar PDP ya je wurin ana sa-in-sa har ta kai ga ya daki wasu daga cikin 'yan kwamitin da gwamna ya kafa.

Wani wanda ya gane wa idanunsa faruwar al'amarin, Jeremiah ya shaida wa BBC cewa "al'amarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar inda matashin a jam'iyyar PDP ya koma kauyensu kuma jama'a suka tarbe shi a otal din Prodest da Alode.

Can da yamma kuma sai kawai 'yan kwamitin yaki da korona suka zo suka ce akwai abun da ke faruwa saboda haka sai an ba su kudi naira 100,000.

Hakan ne kuma ya fusata matashin jam'iyyar PDP inda ya ce ba zai ba su ko da anini ba. Sai suka ce idan har bai ba su abin da suka tambaye shi to za su kai kararsa wurin gwamna Wike kuma sai an rushe otal din.

Abin mamaki sai kawai muka ji wai gwamnati ta ayyana wannan matashi abin nema har ma ta sanya kudi naira miliyan biyar ga duk wanda ya samo shi.

Daga nan kuma sai jami'an tsaro suka zo suka kama manajan otal din kuma suka rushe shi sannan suka rushe karin wani otal bisa zargin cewa sun karya dokar kulle."

Tuni dai gwamnan jihar Rivers din, Nyeson WIke ya ce otal din guda biyu sun karya dokar kulle da gwamnatin jihar ta kafa.

To sai dai mutane da masana harkar shari'a na ta fama tofa albarkacin bakinsu dangane da ko gwamnan na da dama a dokance ta rushe wadannan otal guda biyu.

Ana dai yi wa gwamnoni kallon sanya siyasa a yayin gudanar da al'amuransu a zamanin annobar korona, inda suke cuzguna wa abokan hamayya.