Coronavirus a Kano: Ƙarin Mutum 8 sun kamu, 50 a makwabtanta

Gwamna Abdullahi Ganduje

Asalin hoton, KNSG

Lokacin karatu: Minti 2

Alkaluman hukumomi sun nuna cewa an kara samun masu cutar korona takwas ranar Juma'a a Kano, jihar da ta fi fama da annobar a arewacin Najeriya, da wannan yawan masu cutar 761.

Wannan a iya cewa daya ce cikin ranekun da aka samu adadin mafi kankanta da na mutanen da aka tabbatar sun sake kamuwa da cutar a Kano.

Haka kuma an samu karin mutum uku da suka warke kuma aka sallame su daga asibiti sakamakon korona a Kano. Yanzu adadin mutanen da suka warke a Kano 90 ne.

Kuma ma ba a samu ko mutum guda da ya mutu ba cikin sa'a 24 da ta wuce, don haka har yanzu yawan wadanda cutar ta kashe a Kano 33 ne.

Sai dai kuma alkaluman da hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta fitar sun nuna, yayin da yawan mutanen da suka sake kamuwa da korona a Kano ya ragu, adadin mutum 50 ne suka sake kamuwa a jihohin da suke kewaye da ita.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

BBC
Karin bayani kan coronavirus

Jadawalin jiha 34 da birnin Abuja da cutar ta bulla ya nuna Kano ce har yanzu ta biyu a yawan masu cutar korona da mutum 761, a bayan Legas mai mutum 2,278.

Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Najeriya ta kuma nunar cewa a jihar Kaduna an sake samu mutum 20 da suka kamu, jihohin Katsina da ke yammacin Kano an samu karin mutum 15 ita ma Jigawa da ke gabas 15 din ne suka sake kamuwa.

Gwamnatin Kano dai ta tsawaita dokar kulle da mako guda a kokarinta na shawo kan annobar, ko da yake malaman addini a jihar na ta da a sassauta dokar musamman don ba da zarafin halartar masallatan Juma'a.

Jihohi kamar Jigawa da Borno sun sanar da dage dokar inda suka bai mutane damar halartar sallolin jam'i, musamman na Juma'a da na sallar idi mai zuwa.

Alkaluman da hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Najeriya ta fitar a daren Juma'a sun nuna cewa yawan masu korona a Katsina sun kai 239, Jigawa na da mutum 191, sai Kaduna mai 134.

Ya zuwa daren Juma'a 15 ga watan Mayu, mutum 5,445 ne suka harbu da korona a daukacin Najeriya, cikinsu, 171 sun rasu sakamakon cutar yayin da 1,320 suka warke kuma aka sallame su.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2