Sergio Aguero: 'Yan wasan Premier na fargabar koma wa kwallo
'Yan wasa na jin tsoron koma wa kwallo a lokacin da ake fama da cutar Coronavirus, in ji dan kwallon Manchester City Sergio Aguero.
Ana sa ran za a koma buga gasar Premier a ranar 8 ga watan Yuni, abin da zai sa 'yan wasa su koma horo daga ranar 18 ga watan Mayu.
Manyan kungiyoyi za su tattauna a ranar Juma'a kan batun sake koma wa murza leda.
"Galibin 'yan wasan na jin tsoro saboda suna da iyali da yara," in ji Aguero.
An dakatar da buga gasar Premier ne a ranar 13 ga watan Maris saboda cutar coronavirus amma kuma galibin kungiyoyin na soma a koma buga kwallo a yayin da za su buga wasanni 92 da suka rage.
Ana sa ran za a buga wasannin ba tare da 'yan kallo kuma watakila kyauta za a nuna a gidajen talabijin.







