Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An wayi gari da gawa yashe a gefen titi a Jihar Kano
Wasu al'ummar jihar Kano sun wayi gari tare da wani mutum kwance a gefen titi, wanda ake tunanin gawa ce.
Mazauna kusa da barikin sojoji na Bukavu da ke Kofar Ruwa a Kano sun ce sun samu wani mutum yashe a gefen titi, kuma suna tunanin ya shafe sama da sa'a 24.
Wani mazaunin unguwar ya shaida wa BBC cewa tun a ranar Juma'a suka ga mutumin yana zaune a bakin Titin Katsina.
Ya ce da misalin karfe 11:00 na ranar Asabar ne mutane suka fara taruwa a kansa kuma suka yi amannar cewa ya rasu, inda nan take suka tuntubi jami'an tsaro amma hakansu bai cimma ruwa ba.
"Da farko mun tuntubi 'yan kwana-kwana a Bacirawa sai suka ce yankin bai shafe su ba," in ji shi.
BBC ta tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, kuma ya ce sun samu labarin gawar, amma ya ce kula da gawar ba hakkinsu ba ne, hakkin jami'an lafiya ne.
Mutanen unguwar sun ce sun kai rahoto ofishin 'yan sanda na Dala, inda aka shaida masu cewa sai dai su tuntubi ma'aiakatar lafiya.
"Mun kira lambobin hukumar NCDC amma lambar ta ki shiga," in ji Benjamin, daya daga cikin mazauna unguwar.
Ya kara da cewa daga baya sun je Asibitin Murtala, sun je wurin me Unguwar Dala amma babu wanda ya je wurin gawar.
Ya ce har zuwa karfe 12:30 na ranar Lahadi gawar na nan yashe a gefen titi.
A 'yan kwanakin nan an samu mace-mace a Kano da mazauna jihar ke cewa ba a saba gani ba.
Rahotanni sun nuna cewa an yi rashin manyan mutane da suka hada da manyan malaman jami'a da tsofaffin ma'aikatan gwamnatin jiha da na tarayya.