Coronavirus: Yadda aka raba wa talakawa kayan abinci a Lagos

Wasu kungiyoyin sufuri sun raba wa mutane da masu karamin karfi kayan abinci a wasu unguwannin jihar Legas.

Dubban mutane ne suka fito domin karbar tallafin a Legas da kungiyar masu motocin haya ta RTEAN ta bayar a karkashin shugabanta na kasa Dr. Alhaji Muhammadu Musa Maitokobi.

Wakilin BBC a Legas ya ce kungiyar na rabawa mambobinta matsakaicin buhun shinkafa da naira dubu goma ga kowanne mutum daya.

Ya ce ana bayar da tallafin ne ba tare da nuna bambanci ba tsakanin masu lafiya da kuma masu bukata ta musamman. Kuma ana bin tsarin farkon zuwa farkon samu ba tare da nuna bambanci addini ko kabila a yayin raba tallafin.

An hana fita a Jihar Legas da ke da yawan jama'a a Najeriya kuma inda cutar korona ta fi yin kamari a kasar.

Kuma wakilin BBC ya ce mutane sun yi layi wajen karbar tallafin ba tare da bayar da tazara ba tsakaninsu, kamar yadda ake umurtar mutane su kiyaye don dakile yaduwar cutar.

Miliyoyin mazauna jihar na cewa tallafin da ake cewa an bayar daga gwamnatin tarayya da kuma jihohi bai fara kai wa a gare su ba.

Ga yadda ake rabawa mutane tallafi a Legas

Karin labaran da za ku so ku karanta