Abba Kyari: Na yi rashin babban amini – Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana marigayi Abba Kyari a matsayin babban amininsa na hakika kuma mai kishin kasa.

Cikin wata sanarwa da shugaba Buhari ya fitar mai taken 'zuwa ga abokina Abba Kyari' ya ce amininsa ne tun shekaru 42 da suka gabata kafin daga baya ya zama shugaban ma'aikata a fadarsa.

A ranar Juma'a ne Allah Ya yi wa Malam Abba Kyari rasuwa yana da shekara 67 a duniya bayan ya yi fama da cutar korona.

Shugaba Buhari ya ce Abba Kyari wanda ya fara haduwa da shi tun yana saurayinsa dan shekara 20, "bai taba yin kasa a gwiwa ba wajen sadaukar da kai ga ci gaban kowannenmu ba."

"Abba Kyari, mutumin kwarai ne da ya fi mu," in ji Buhari.

Ya kuma ce kasancewar Abba Kyari shugaban ma'aikata a fadarsa a 2015, "ya yi iya kokarinsa ba tare da nuna kansa ba ko neman mallakar abin duniya wajen aiwatar da burina ba."

Shugaban ya bayyana Abba Kyari a matsayin tsayayye kan lamurran da suka shafi fadarsa. "Yana aiki ba gajiya, dare da rana, wajen tabbatar da babu wanda - ko minista ko gwamna da zai wuce gona da iri a fadar shugaban kasa da kuma dukkanin wakilai da wadanda ke yi wa kasa aiki sun samu dama ba tare da nuna fifiko ko bambanci ba.

Ya kuma ce Abba Kyari a rayuwarsa ta siyasa bai taba neman tsayawa takara ba don neman mukami ba. maimakon haka mutum ne mai adawa da irin dabi'un tsarin siyasar Najeriya na yanzu - wadanda suka rungumi rashawa da kuma alfanunta na samun mukamin siyasa.

Daga karshe Shugaban ya mika sakon ta'aziyarsa ga iyalan marigayi Abba Kyari kan babban rashin da suka yi.