Coronavirus: Yadda ya kamata a yi jana'iza a Musulunci lokacin annoba

Asalin hoton, PA Media
Ana bayyana fargaba kan hanyoyi da matakan da ya kamata a bi wajen binne mutanen da cutar korona ta kashe.
Hukumomi a Najeriya sun dauki mataki na hana duk wani taron jama'a har da Sallar jam'i da tilasta hana fita da kwadaitar da bayar da tazara tsakanin mutane, amma wasu na ganin akwai kura-kurai da dama da suka faru yadda aka gudanar da jana'izar marigayi Malam Abba Kyari, shugaban ma'aikata a fadar shugaban kasar.
Daga cikin wadanda suke ganin an saba doka da umarnin masana kiwon lafiya da kuma tanadin da musulunci ya yi idan ana cikin annoba sun hada da Babban limamin masallacin juma'a na Nagazi-Uvete da ke Okene, Jihar Kogi Imam Murtadha Muhammad Gusau.
Malamin ya bayar da fatawa kan yadda ya dace a yi jana'aiza a musulunci lokacin da ake cikin annoba.
Malamin ya ce ya kalli yadda aka yi jana'izar Abba Kyari kuma a cewarsa, "tun daga yadda manyan jami'an gwamnati, har da na fadar shugaban kasa, suka yi cincirindo a filin jirgin sama domin tarbon gawarsa, bai dace ba."
Ya ce hakan ta faru duk da ana sane da irin gargadi da jan kunne da jami'an lafiya da kuma hukumar da ke kula da cututtuka masu yaduwa, NCDC ke yi na kauracewa cunkoson jama'a don dakile yaduwar cutar..
"Mutum biyu ya kamata a ce sun tarbi gawar, duba da irin halin da ake ciki na yaduwar wannan annoba, amma ba kamar yadda jami'an gwamnati da dama, da wasu ma'aikata suka taru tun daga filin jirgi har zuwa makabarta ba," in ji Malamin.
Imam Murtadha Muhammad Gusau ya bayyana irin tanadin da musulunci ya yi na jana'iza a lokacin yanayi na annoba kamar haka:
Wankan gawa
Game da wanke mamaci, ba dole ba ne sai mutane sun sa kansu cikin matsalar cewa dole sai an yi masa wanka irin na asali. Addinin musulunci sauki ne da shi, bai tsananta ba. Duk abin da ake yi wa mamaci, idan har akwai tsoro ko yiwuwar kamuwa da cutar, to ana iya barin sa.
Idan har ba za a yi wankan gawar ba da ruwa saboda cutar corona, ana iya yin taimama da kasa maimakon ruwa.
Za a shafa kasa a shafe fuskar mamaci, sai hannayensa, daga nan a sa masa likkafani, a yi masa Sallar Janaza a binne shi (A diba Majmu'u Fatawa wa Maqalat Mutanawwi'ah, Kundi na 13, shafi na 123 na Shaikh Abdul-Aziz Bin Baz da Fatawa fi Ahkam Al-Jana'iz na Shaikh Muhammad Bin Salih Al-Uthaimin, shafi na 213-214]
Idan kuma babu damar yi masa wanka saboda annobar Korona, ana iya lullube gawar da likafani, a yi wa gawar Sallah a binne. Wannan saboda Manzo SAW ya umurci a gaggauta kawar da mamaci kada a yi jinkiri. [Bukhari].
Idan kuma annobar cutar Korona ba ta haramta taba jikin mamaci ba, ko da safar hannu, wannan ba zai hana a yi masa dukkanin abin da ya kamata a yi wa musulmi ba da ya rasu.
Babu kyau a jinkirta binne mamaci na kwanaki ko watanni, don a jira har sai hukumomi sun dage dokar takaita fita saboda an fi son a gaggauta kawar da mamaci.
Idan kuma gawar ta kasance a rufe cikin jika, kuma dokar da hukumomi suka kafa ba ta bayar da damar budewa ba, don haka wankan gawa ba zai samu ba. Bisa haka ana iya lullube gawar da likafani a yi wa gawar sallah a binne ta [A diba Majmu'u Fatawa wa Maqalat Mutanawwi'ah, kundi na. 13, shafi na 128-129 na Shaikh Abdul-Aziz Bin Baz]
Sallar Jana'iza

Asalin hoton, PA Media
Malamin ya ce taruwar da aka yi wurin jana'izar marigayi Malam Abba Kyari, wannan bai dace ba ace kusan mutum hamsin sun taru domin yi masa jana'izah.
A cewarsa, "Mutum uku-hudu-biyar-bakwai sun isa. Wannan kuwa ba domin komai ba sai domin kokarin kiyaye kai. Kuma irin yadda mutane suka tsaya, ba tare da wata rata mai nisa tsakaninsu ba, suka yi masa sallah, shi ma wannan an yi kuskure,"
"Saboda su jami'an gwamnati ya kamata su zama abun koyi ga sauran gama-garin mutane, ba sune zai zama kuma suna saba dokokin da aka shinfida ba,".
"Sannan idan mun lura, a makabarta wurin binne shi, irin yadda mutane suka taru a makabartar, domin yin rakiya ga gawar, da irin yadda mutane suka rungumi gawarsa wurin sa shi cikin kabari, duk an tabka kuskure, la'akari da irin halin da ake ciki na yaduwar wannan annoba cikin gaggawa,"
"Idan har dokar hana fita da aka kafa kan cutar Korona ta hana jam'in Sallar jana'iza, ko da kuwa makusanta ga mamacin ne, to ya halatta wasu mutane kalilan su hadu su yi wa mamacin Sallah su kuma binne shi,"
Wadanda kuma ba su samu sallar ba suna iya kai ziyara kabarinsa su yi masa addu'a. [A diba Majmu'u Fatawa wa Maqalat Mutanawwi'ah, Kundi na. 13, shafi na 153 na Shaikh Abdul-Aziz Bin Baz]
Musulmi suna iya yin sahu uku bayan Liman. Kamar yadda Abu Umamah ya ruwaito.
"Annabi Muhammad SAW ya taba yin Sallar Jana'iza kuma mutum bakwai ne kawai a bayansa. Ya sa mutum uku a sahu na gaba, biyu kuma a wani sahu, sai biyu a sahu na uku." [At-Tabarani a cikin Al-Kabir, kuma Imamul Al-Albani ya inganta shi a cikin Ahkam Al-Jana'iz, shafi na 127].
Idan hukumomi ne suka binne mamacin ba tare da an yi masa sallah ba, musamman idan kasashen da ba na musulmi ba ne, musulmi na iya tambayar inda kabarinsa yake sai su yi masa Sallah kamar yadda aka bayyana.
Idan kuma ba a san inda aka binne shi ba, za a iya yi masa Sallar Jana'iza ba sai da gawarsa ba, kamar yadda Manzo SAW ya yi wa Najjashi Sarkin Abyssinia. A wannan yanayin, ana yin Sallar Jana'iza kamar yadda ake yi, kawai gawar mamacin ce kawai babu a gaban liman.
An amince a yi Sallar Jana'iza a dakin da aka yi wa mamaci wanka, amma a haraba, wajen Masallaci ya fi, ko da yake babu komi idan an yi a Masallaci [A diba Majmu'u Fatawa wa Maqalat Mutanawwi'ah, kundi na 13, shafi na 157 da kuma kundi na 13, shafi na 164 na Shaikh Abdul-Aziz Bin Baz]
Idan za a yi wa mamaci Sallah, ana yin sahu kamar yadda ake yin sallah. Amma idan annobar cutar korona ta hana yin haka, to sai a bayar da tazara tsakanin mutanen da ke sallar.
Binne mutum fiye da daya
An amince a binne mutum fiye da daya a kabari daya idan akwai bukatar haka, musamman a yanayin da aka samu gawawwakin wadanda suka mutu da yawa, kuma wurin da za a binne su ya yi karanci.
A wannan yanayin, musulmin da ya fi sanin Al Qur'ani mai tsarki ake fara saka wa a farko kusa da al kibla a kabarin, kuma ana jera su kusa da juna. Malamai sun kuma bayyana cewa tsakaninsu ana sa shamaki. [A diba Fatawar Ahkam Al-Jana'iz na Shaikh Muhammad Bin Salih Al-Uthaimin, shafi 213-214]


Bai dace a bayar da gawar mamaci ba
Malamin ya bayyana cewa "ya kamata gawar mamacin da ya rasu saboda cutar annobar kurona, bai kamata a hannunta ta ga masu ita ba, wai don yi masa jana'izah. Ko kuma a bari wai 'yan uwan mamacin su halarci jana'izar sa, ko ace dole sai sun gan shi,"
"Dukkaninmu mun sani, babu abin da mamaci yake bukata daga wurin mu illa addu'a,""Idan musulmi ne, hukumomi su shirya masa jana'izah ta musulunci su binne shi. Idan kirista ne, hukumomi su shirya masa jana'izah irin ta kirista su binne shi, idan dai har da gaske ake yi wurin yaki da wannan annoba,"
"Ya kamata wani abin da ya faru a kasar Amurka ya zama izina da darasi a gare mu, yadda wasu mutane suka taru suka yi jana'izar dan uwansu da cutar annobar korona ta kashe, amma bayan sun gama jana'izar aka gwada su, sai aka tarar duk sun kamu da wannan cuta, kuma ma sun yada ta zuwa ga wasu. Don haka sai mu kiyaye,""Wannan shi ne dan abin da zan ce, ina mai rokon Allah kiyaye mu, kuma ya sa mu dace, amin," kamar yadda Imam Murtadha Muhammad Gusau, babban limamin masallacin juma'ah na Nagazi-Uvete da ke Okene, Jihar Kogi ya bayyana.











