'Yan Najeriya mazaunan Dubai sun roki a dawo da su gida

Wasu 'yan Najeriya da dokar hana fita ta rutsa da su a birnin Dubai na hadaddiyar Daular Larabawa sun roki gwamnatin kasarsu ta gaggauta taimaka musu a dawo da su gida.

Daya daga cikinsu, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce yanzu sun kwashe kimanin makonni hudu suna rufe rif a gidaje, yayin da wasu kasashe ke ci gaba da kwashe jama'arsu.

Ya ce, ''Akasari kasuwanci ne ya kai mu, sai annobar cutar korona ta rutsa da mu kusan mako 4 zuwa 5, gashi ba ma samun damar iya ko motsawa''.

Mutumin ya ce duk da cewa har yanzu babu wani gwajin da aka musu wanda hakan zai ba su damar koma wa gida, makonnin da suka kwashe killace ya isa kafa hujjar cewa kalau suke.

''Takaita zirga-zirgar da aka yi, ya hana mu isa ofishin jakadancin Najeriya da ke Abu Dhabi, wasu na yawan cewa za a kwashe mu cikin kwanaki 10 amma har yanzu shiru" inji mutumin.

'Yan Najeriyar dai sun koka da yanayin da suka tsinci kansu tare da bayyana yadda suke kewar 'yan uwa da iyalansu.

Dubai dai cibiyar kasuwanci ce a duniya inda 'yan kasashe da dama ke zuwa domin saye da sayarwa, sai dai lamura sun tsayawa kasar cak a yanzu saboda annobar cutar korona.

Kafin wannan lokacin kasar ta Hadaddiyar Daular Larabawa na karbar milyoyin baki a rana guda da ke hada-hada.

Najeriya na daya daga cikin kasashen da ke yawaita ziyarta kasar domin cinikayya.

Wannan annoba ba wai Dubai kawai ta shafa fa, hatta tattalin arzikin kasashe da dama ya durkushe cikin dan kankanin lokaci tun bayan bularta.

Asusun lamuni na IMF ya bayyana durkushewar tattalin arzikin a matsayin mafi muni tun matsin tattalin arziki da aka shiga a duniya a shekarun 1930.

Sannan ya kara da cewa idan annobar ta dade ba a shawo kanta ba, gwamnatocin kasashe da manyan bankunan kasashe za su wahala kafin su farfado da tattalin arzikin.

Shi ma Bankin Duniya ya yi gargadi kan jama'ar da suka dogara kan masana'antu da cewa suna cikin babban hadari sakamakon tasirin da cutar za ta yi.

A wani hasashe da ya yi, bankin ya ce idan abubuwa ba su tabarbare sosai ba kusan mutum miliyan 24 za su tsallake fadawa talauci a yankin a shekarar 2020, sakamakon tasirin da annobar za ta yi ga tattalin arziki.