Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Duniya za ta shiga matsin tattalin arziki mafi muni cikin shekara 90
- Marubuci, Daga Szu Ping Chan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Business reporter, BBC News
Tattalin arzikin duniya zai ragu da kashi uku cikin 100 a wannan shekarar, yayin da na kasashe a fadin duniya ke raguwa cikin saurin da ba a taba ganin irinsa ba a baya-bayan nan, in ji Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, IMF.
IMF ya bayyana durkushewar tattalin arzikin a matsayin mafi muni tun matsin tattalin arziki da aka shiga a duniya a shekarun 1930, wato Great Depression.
Asusun ya ce annobar ta jefa duniya cikin "rikicin da bai da tamka".
Sannan ya kara da cewa idan annobar ta dade ba a shawo kanta ba, gwamnatocin kasashe da manyan bakunan kasashe za su wahala kafin su farfado da tattalin arzikin.
Gita Gopinath, babbar jami'a a bangaren tattalin arziki a IMF ta ce matsin da aka shiga zai wawure dala tiriliyan tara daga arzikin da aka samar a duniya a shekara biyu masu zuwa.
'Komai ya tsaya cik'
Yayin da rahoton IMF kan tattalin arzikin kasashen duniya ya yabi kasashe kamar Burtaniya da Jamus da Japan da Amurka kan matakan gaggawa kuma masu ma'ana da suka dauka, rahoton ya ce babu kasar da za ta gujewa durkushewar tattalin arziki.
Yana sa rai tattalin arzikin duniya zai gyaru da kashi 5.8 cikin 100 a shekara mai zuwa idan annobar ta bace a watanni shidan karshe na shekarar 2020.
Ms Gopinath ta ce dakatar da ayyuka da kasuwanci da zirga-zirga cik mummunar alama ce ga masu kirkirar manufofi, wadanda ke fuskantar "rashin tabbas kan girmar barnar da annobar za ta yi."
"Ana sa rai za a samu sauki a shekarar 2021," in ji Ms Gopinath. "Amma yawan arzikin da aka samar zai zauna a matsayin da yake kafin annobar ta bullo, kuma babu tabbas kan yadda karfin tattalin arzikin zai kasance idan ya habako.
Lamarin ya shafi duka duniya
Ms Gopinath ta ce a karon farko tun bayan matsin tattalin arziki na shekarun 1930, ana sa rai kasashen da suka ci gaba da masu tasowa duk za su fusknaci durkushewar tattalin arziki.
IMF ta yi gargadin cewa ba za a ga ci gaba a tattalin arzikin kasashen da suka ci gaba ba sai a kalla nan da shekarar 2022.
Ana sa rai tattalin arzikin Amurka zai ragu da kasha 5.9 cikin 100 a wannan shekarar, kuma wannan shi ne durkushewarsa mafi girma a shekara tun 1946. Haka kuma, ana sa rai rashin aikin yi a Amurka zai karu da kashi 10.4 cikin 100 a wannan shekarar.
Ana sa rai a shekarar 2021 tattalin arzikin zai dan farfado, kuma a Amurka zai farfado ne da kashi 4.7 cikin 100.
Ana sa rai tattalin arzikin China zai karu da kashi 1.2 cikin 100 kawai a wannan shekarar, kuma shi ne girman tattalin arzikinta mafi karanci tun 1976.
Karin labaran da za ku so ku karanta
Australiya za ta fuskanci durkushewar tattalin arzikinta tun 1991.
IMF ta yi gargadin cewa akwai "munanan hadurra kan yadda tattalin arzikin zai zama".
Ya ce idan annobar ta dade ba a shawo kanta ba kuma aka sake samun barkewarta a 2021, wannan zai sake rage kashi 8 cikin 100 na gaba daya arzikin da aka samar a duniya.
Asusun ya ce wannan na iya jawo wa kasashen da suke da yawan bashi mummunan koma baya.
Ya ce masu zuba jari ba za su so su sake bai wa wadannan kasashe bashi ba, kuma wannan zai kara dagula lamarin.
IMF ya kara da cewa: "Wannan karin da za a samu a farashin kudin da ake arowa na iya hana kasashe da yawa samar da kudin rage radadin talauci da ake so a samar.
Mafita
Yayin da dakatar da ayyuka cik zai matsa wa ayyukan kasuwancin kasashe, IMF ya ce killacewa da barin tazara na da matukar muhimmanci.
Ya ce: "Matakan hana yaduwar cutar na da muhimmanci kuma za su bai wa asibitoci da cibiyoyin lafiya damar iya kula da marasa lafiya kuma suna taimakawa wajen samar da hanya nan da nan da za a dawo da ayyukan kasuwanci.
IMF ta jera hanyoyi hudu mafi muhimmanci na shawo kan annobar.
Ya yi kira da a kara sa kudi a bangarorin kiwon lafiya, a bai wa ma'aikata da sana'o'i tallafin kudi, babban bankin kasa ya ci gaba da ba da tallafi sannan a samu tsari mafi dacewa wajen habako da tattalin arzikin.
Ya bukaci kasashe su yi aiki tare wajen ganowa da rarraba magunguna da riga kafi.
Asusun ya kara da cewa kasashe masu tasowa da yawa za su bukaci a biya masu basukansu a watanni da shekaru masu zuwa.