Yadda sojojin Chadi 'suka kashe 'yan Boko Haram' 1,000

an kashe dakarun Chadi 52 a bata-kashin da aka kwashe kwana shida ana yi a tsakaninsu.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An kashe dakarun Chadi 52 a bata-kashin da aka kwashe kwana shida ana yi a tsakaninsu

Rundunar sojin Chadi ta ce ta kashe mayakan Boko Haram 1,000 a wani samame da ta kai yankin Tafkin Chadi.

Kakakin rundunar sojin Kanar Azem Agouna ya ce an kashe dakarun Chadi 52 a bata-kashin da aka kwashe kwana shida ana yi a tsakaninsu.

Shugaba Idriss Déby ya ziyarci yankin Tafkin na Chadi. Ya ce babu dan kungiyar Boko Haram ko daya da ya rage a yankin.

Ya yi takaici kan yadda ya ce an bar Chadi ita kadai take fatattakar mayakan na Boko Haram a fadin Tafkin na Chadi, wanda ke da iyaka da kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi.

An kaddamar da farmakin ne bayan da a watan jiya sun kashe dakarun Chadi kusan 100 a harin da suka kai musu a yankin.

Har yanzu dai babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da ikirarin sojojin Chadin kuma Boko Haram bata ce komai ba.

Mayakan Boko Haram suna da mafaka a yankin Tafkin Chadi

Asalin hoton, BOKO HARAM VIDEO

Bayanan hoto, Mayakan Boko Haram suna da mafaka a yankin Tafkin Chadi