Covid-19: 'Za a kai lokacin da mutane za su soma faduwa suna mutuwa a Najeriya'

Masana harkar lafiya a Najeriya sun fara nuna damuwa kan yadda jama'a ke daukar batun coronavirus, inda suke kunnen kashi da shawarwarin da jami'an lafiya ke bayarwa.
Farfesa Usman Yusuf wanda shi ne tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta Najeriya ya ce abin da suke gani yana tayar wa da duk wani masanin harkokin lafiya hankali.
Farfesa Usman ya shaida wa BBC cewa idan jama'a ba su sauya yadda suke daukar cutar ba, to za ta iya yin mummunar illa.
Ya ce hankalin likitoci a Najeriya da na kasashen ketare a tashe yake, domin sun ga yadda ta fara a China, inda dimbin jama'a suka rasa rayukansu daga nan ta bazu kasashen duniya.
"Ta zo Italiya da Spain yanzu tana Ingila har da shugabansu, Firai minista yana dauke da wannan cuta."
Ta yadu Amurka, kuma duk kudinta da bama-bamanta amma cutar ta gagare ta, mutane sai mutuwa suke inda ake mayar da filayen wasanni asibiti."
"Amma mu a nan Najeriya, jama'a ba a dauke ta da muhimmacin da ya kamata ba, shi ya sa hankalinmu ya tashi, saboda yadda muke jin jama'a na cewa ai ba ta kawo nan ba, ba ta zo arewa ba," in ji Farfesan.


Ya ce duk wadannan maganganun da mutane ke yi ba gaskiya ba ne, domin duk kasashe akwai lokacin da kwayar cutar ke bunkasa a kasa idan jama'a ba su bayar da goyon baya ba.
"Idan jama'a ba su fahimci hatsarin da ke tattare da cutar ba haka za a ta yin abubuwa mutane na faduwa suna mutuwa."
Ya yi kira ga jama'a da gwamnati cewa a kara daukar matakai kada har a kai lokacin da jama'a za su fara faduwa a masallatai ko kasuwanni, ana zuwa asibiti, kuma tana kama likitoci.
Zuwa yanzu adadin mutane 238 da aka tabbatar sun kamu da coronavirus a Najeriya, inda 35 daga cikinsu suka warke, yayin da kuma cutar ta kashe mutum biyar a kasar.
Latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraron hirar Farfesa Usman Yusuf da Yusuf Yakasai na BBC:
Karin labaran da za ku so ku karanta












