Coronavirus: Yadda na warke daga cutar a Nigeria

Infographics of woman with facemask looking at her tablet

Wani bawan Allah da ya warke daga cutar coronavirus a Najeriya ya ce a lokacin da likitoci suka fara shaida masa cewa ya warke da coronavirus kasa gaskatawa ya yi.

Mutumin muka boye sunansa saboda tsaro, ya shaida wa BBC cewa ya shafe kwana 14 a babban asibitin kwararru da ke Gwagwalada a babban nirninbtrayyar Najeriya Abuja.

A makonni biyun da suka wuce ne likitoci suka ce masa yana dauke da cutar coronavirus bayan dawowarsa daga Burtaniya, amma kuma a gwajin baya-bayan nan an sake gwada shi ba ya dauke da cutar.

''Abin da ya faru shi ne na dawo daga tafiya ranar Juma;a sai na ce bari na kaurace kamar yadda jami'an lafiya ke ta gargadi, a ranar Asabar kuma sai na kira hukumar NCDC suka zo suka dauki samfuri don yi gwaji,'' in ji shi.

Bayan kwana biyu da yin gwajin ne sai hukumar NCDC ta kira shi a ranar Litinin ta ce masa gwajin ya nuna yana dauke da cutar, ''sai na ce Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, saboda faduwar gaba. Sai na ce to mene ne abin yi a yanzu?

Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus

''Sai suka ce min za su zo su kai ni cibiyar da ake killace mutanen da ke dauke da cutar a Gwagwalada. Sai na ce Alhamdululillah. Daga nan na yi mai dakina bayani na kuma ce mata ashe gara da na killace kaina bayan dawowar tawa.

''Dama tun da na dawo na zauna wajen iyalina ba,'' a cewarsa.

Latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraron cikakkiyar hirarsa:

Bayanan sautiHira da wanda ya warke daga coronavirus a Najeriya

Yadda ta kasance a Gwagwalada

Mutumin ya ce a ranar farko da washe gari ya samu kansa cikin tunani iri-iri na yadda kullum ana kallon yadda cutar take a talbijin da waya da hanyoyin sada zumunta cewa tana kisa, ''to tsoro ya kama ni.''

''Amma bayan kwana biyu da likitocin, wadanda kwararru ne suka yi mana bayani suka ce cutar nan ba wai kabari salamu alaikum ba ce, ana warkewa, sai hankalina ya kwanta.''

Gwamnati ta cancanci yabo

Ya kara da cewa yanayin yadda cibiyar killace mutanen take abin a yaba wa gwamnati ne ''duk kuwa da cewa ba komai da kake bukata ne za ka samu a asibiti ba.

''Za ka ga cewa kowane marar lafiya da dakinsa daban sannan akwai na'urar sanyaya daki.

Kan batun bayar da magani kuwa ya ce tun a ranar d aka zo za a ba ka magunguna irin yadda ya dace da yanayin mutum. ''Likitocin sun ce akwai masu nuna tsananin rashin lafiya, da masu saisa-saisa da kuma wadanda ba sa nuna komai.

''To ni ma dai har yanzu da na yi kwana 14 a wajen killace masu cutar ban nuna wata alama ba sam-sam. Kuma da aka sake yi min gwaji likita ta ce a yanzu ba na dauke da cutar sai da na yi tantama na ce gaskiya likita kin tabbatar kuwa? Ta ce kar na damu daidai gwajin ya nuna,'' in ji shi.

Wannan layi ne

Karin labaran da za ku so ku karanta

Wannan layi ne