Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Covid-19: Amurka ta soma kwashe 'yan kasarta daga Najeriya
Amurka ta soma kwashe 'yan kasarsa daga Najeriya a yayin da duniya ke ci gaba da fama da annobar coronavirus.
Sanarwar da ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Talata, ya ce tun ranar Litinin aka kwashe Amurkawa 376 daga kasar zuwa birnin Washington.
Ofishin ya kara da cewa za a ci gaba da kwashe Amurkawa daga Najeriya zuwa Washington.
A makon jiya Amurka ta sanar cewa za ta soma kwashe 'ya'yanta daga Najeriya, jim kadan bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da rufe jihohin Lagos da Ogun da kuma babban birnin tarayya Abuja.
Alkaluma dai sun nuna cewa coronavirus ta fi yin illa a Amurka inda ya zuwa ranar Talata mutum fiye da 360, 000 suka kamu da cutar yayin da mutum sama da 10,000 suka mutu.
A Najeriya, alkaluma sun nuna cewa mutum 238 ne suka kamu da cutar yayin da mutum biyar suka mutu.