Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kusoshin gwamnati da suka kamu da coronavirus a Najeriya
Tun dai ranar 27 ga watan Fabrairu wato ranar da cutar coronavirus ta fara bulla a birnin Legas na Najeriya, bayan zuwan wani dan kasar Italiya birnin, 'yan kasar ke ta kasa kunne domin jin wane ne zai kamu a gaba.
Wannan cuta ta coronavirus ta harbi shugaban ma'aikata a fadar gwamnatin Najeriya da akalla gwamnoni guda uku na kasar da kuma shugaban hukumar kula da shige da fici ta Najeriyar.
Ga wasu daga cikin kusoshin Najeriya da cutar ta harba.
- Abba Kyari - Shugaban Ma'aikata a fadar gwamnatin Najeriya
- Bala Muhammad - Gwamnan Bauchi
- Nasir El-rufa'i - Gwamnan Kaduna
- Seyi Makinde - Gwamnan Oyo
- Muhammad Babandede - Shugaban hukumar kula da shige da fice
Abba Kyari - Tun dai lokacin da fadar gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa Malam Abba Kyari ya kamu da cutar coronavirus, har kawo yanzu ba a kara jin duriyarsa ba. Rahotanni na cewa shugaban na ma'aikata a fadar shugaban Najeriyar ya kai ziyarar aiki kasar Jamus ne, ranar 7 ga watan Maris kuma ya koma Najeriya ranar 14 ga watan na Maris, ko da yake a lokacin bai nuna alamun rashin lafiya ba.
Sai dai masu sharhi na ganin ya kamata tun lokacin da ya koma Najeriya ya killace kansa domin yin biyayya ga umarnin da gwamnatin kasar ta yi cewa duk mutumin da ya koma kasar, to ya killace kansa tsawon mako biyu kafin ya soma gana wa da jama'a.
Hasalima, wasu rahotanni sun ce tun lokacin da ya koma gida, Abba Kyari ya halarci taruka daban-daban kan matakin da gwamnati take dauka domin shawo kan cutar ta COVID-19.
Bala Muhammad
Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya kamu da coronavirus bayan da sakamakon gwajinsa ya fito.
Wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar mai dauke da sa hannun babban mai bai wa gwamnan shawara kan yada labarai Mukhtar M Gidado, a ranar 24 ga watan Maris ce ta tabbatar da hakan.
Tun lokacin ba a sake jin duriyarsa ba sai a makon nan a cikin wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta, inda gwamnan ya ce yana cikin koshin lafiya kuma idan ya koma jiharsa zai kara zama gwamna mai adalci.
Nasir El-rufa'i
Tun bayan da gwamnan na Kaduna, Nasir El Rufai ya sanar da cewa ya kamu da cutar coronavirus a ranar 28 ga watan Maris, ba a sake ganinsa a zahiri ba yana aiwatar da wani abu.
Sai dai ya halarci zaman majalisar koli da aka yi a kasar a tsakiyar mako, ta hanyar bidiyo kol.
El rufa'i dai ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa yana dauke da cutar coronavirus. Sai dai gwamnan ya ce har lokacin bai fara nuna alamun cutar ba amma ya killace kansa.
"A farkon makon nan ne na yi gwajin cutar Covid-19, kuma sakamakon ya fito a yammacin yau. Ina mai bakin cikin shaida muku cewa ina dauke da cutar," in ji El-Rufai.
"Kamar yadda hukumomin lafiya suka tsara kan abin da mai dauke da cutar ya kamata ya yi, na killace kaina. Mataimakiyar gwamna za ta ci gaba da jan ragamar kwamiti na musamman kan Covid-19 sannan zan ci gaba da bayar da bayanai lokaci zuwa lokaci."
Seyi Makinde
Shi ma gwamnan jihar Oyo da ke kudancin Najeriya, Seyi Makinde ya sanar da cewa ya kamu da cutar coronavirus a ranar 30 ga watan Maris.
Gwamnan wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter, ya ce zai killace kansa kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta bukata.
To sai dai sabanin wasu kusoshin gwamnatin da ba a jin kansu, Gwamna Makinde yana ta wallafa bayanai a shafinsa na Twitter.
Muhammad Babandede
Shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriya, Muhammad Babandede na daya daga cikin manyan jami'an gwamnati da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya. Babandede ya sanar da cewa zai killace kansa na makonni biyu kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta umarta.