Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
West Ham za ta dauko Braithwaite
West Ham na shirin bayar da mamaki inda ta ware £15m domin sayo dan wasan Barcelona da Norway Martin Braithwaite, mai shekara 28, wanda sau uku kawai ya buga tamaula tun da ya koma Nou Camp a watan Janairu. (Mail)
Borussia Dortmund na dab da yin nasara wurin sayo dan wasan Birmingham City mai shekara 16 Jude Bellingham.(Bild, via Birmingham Mail)
Dan wasan Ingila Marcus Rashford ya amince cewa ya zaku ya fafata da abokinsa dan wasan Borussia Dortmund Jadon Sancho, mai shekara 20, a Manchester United a bazara mai zuwa. (Sun)
Manchester United na sanya ido kan halin da Thomas Meunier ke ciki a Paris Saint-Germain a daidai lokacin da babu tabbas kan makomar dan wasan gaban mai shekara 28 dan kasar Belgium. (90min.com)
Kocin Everton Carlo Ancelotti ya ce yana son sake hadewa da dan wasan Real Madrid dan kasar Colombia mai shekara 28, James Rodriguez. (Mirror)
Babban burin dan wasan Manchester United da Faransa Paul Pogba shi ne ya koma Real Madrid idan aka bude kasuwar musayar 'yan kwallon kafa, saboda yana son cika burinsa na haduwa da Zinedine Zidane. (90min.com)
Dan wasan tsakiya na Chelsea Willian ya ce Liverpool ta yi sama sosai a kan teburin Gasar Firimiya ne saboda bata sauya kocinta ba tun 2015. (ESPN Brazil)
A gefe guda, dan kasar Brazil Willian, mai shekara 31, yana iya sake hadewa da tsohon kocin Chelsea Maurizio Sarri a Juventus idan kwangilarsa ta kare a Stamford Bridge a bazara. (Tuttosport)
Middlesbrough na son dauko dan wasan abokan hamayyarsu Sheffield Wednesday Morgan Fox, mai shekara 26. (Yorkshire Post)
Leeds United za ta sayo golan Faransa Illan Meslier, mai shekara 20, a kwangilar dindindin daga kungiyar da ke buga gasar Ligue 1 Lorient idan suka samu daukaka zuwa matakin Gasar Firimiya. (Mirror)