Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus 'ta hana yin shagali a bikina a Kano'
- Marubuci, Halima Umar Saleh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
Coronavirus ba lafiya kawai ta shafa ba, sannan ba fargaba da tashin hankali kadai ta sa mutane a ciki ba, wannan annoba har walwalar mutane ta shafa.
Ga duk wanda ya san yadda rayuwa take a arewacin Najeriya, ya san shagulgulan biki na daya daga cikin manyan hanyoyin da al'umma ke haduwa don taya juna farin ciki da kuma yin zumunci.
Daga watan Janairun kowace shekara har akai watan karshe na Disamba da wuya a samu makon da ba a shagalin biki a wasu sassan kasar, sai dai idan aka dauke watan Azumin Ramadan, sai kuma makonnin Sallah Babba da Sallah Karama.
A shekarun baya-bayan nan, shagalin biki a arewacin Najeriya musamman garuruwa irin su Kano da Abuja da Kaduna, mutane kan kashe miliyoyin kudi don kawata bukukuwa, kama daga kama wajen yin liyafa da kwalliyar amare da abincin da za a ci.
Amma a wannan karon, annobar coronavirus ta hana mutane yin shagalin yadda aka saba.
Wasu sun daga bukukuwan nasu, yayin da wasu kuwa suka yi su haka salin-alin ba taro ba hidima.
'Ban ji dadi ba amma hakan alkhairi ne'
Wata amaryar da aka daura aurenta ranar Juma'a 27 ga watan Maris da na yi hira da ita ta ce min ta yi shiri na yin shagali sosai kuma kawayenta sun yi anko, amma daga bisani sai hakura aka yi da komai aka daura aure ta tare.
Aisha Auwal ta ce duk da cewa ba ta ji dadi da bikinta ya zo a haka ba, amma kuma kiyaye lafiyar jama'a da bin dokokin hukumomi su ne gaba da komai, ''don a matsayina ta likita na san muhimmancin kiyaye lafiyar al'umma dole na zama a bar koyi.
''Bayan hakan ma kuma mutum ya tsira da kudaden da tuni yanzu ya kashe su wajen shagali,'' in ji ta.
Amma kamar ta koka kan yadda wasu masu wuraren yin liyafa suka ki mayar musu da kudadensu da suka fara biya don tanadin wajen, ''tun da dai lamari ne da ba daga wajen mu aka samu akasi ba.
''Mataki ne da hukumomi suka dauka to don me za a ce kuma ba za a dawo mana da kudadenmu ba?'' kamar yadda Aisha ta koka.
'Shagali hudu na shirya yi'
Sadiq Abdullateef ma wani ango ne da ya angwance da amaryarsa a ranar 27 ga watan Maris ne 2020, sai dai aure kawai aka daura ba tare da yin wata hidima ba kamar yadda suka shirya.
''Akalla mun shirya yin hidima guda hudu kuma har mun biya kudaden abinci da na wajen da za a yi shagalin, amma sai gwamnatin jihar Kano ta ba da umarnin rufe dukkan wuraren da ake shagulgulan biki.
''Wannan dalili ne ya sa muka hakura da komai, sai aka daura aure kawai ranar Juma'a bayan idar da Sallar Juma'a. Da yamma kuma mutane kailan suka raka marya, in ji Sadiq.
Sai dai ba kamar yadda wasu suka dinga daga nasu bikin ba, Sadiq ya ce ''babu amfanin daga bikin nan don daurin aure dama shi ne abin da ya zama wajibi. Duk sauran shagukguka bidi'a ne.
''To me ya sa za a daga aure don kawai ba a samu damar yin abin da bai zama ginshiki ba a auren? Ai kowane lamari halaccinsa ake dubawa, wannan abu Allah ne Ya kawo shi don haka babu amfanin dage aure kawai saboda yin liyafa.''
Shi kansa daurin auren da ranar Asabar 28 ga Maris za a yi shi, amma saboda sanarwar rufe Kano da gwamna ya bayar sai aka yi maza aka mayar da shi ranar Juma'a.
''A haka din ma sai da aka sauya wajen da za a yi har sau hudu kafin daga bisani aka samu aka daura a Masallacin Al-Furqan.''
Karin labaran da za ku so ku karanta
'Sana'o'inmu sai abin da hali ya yi'
Ga amare da angwaye a iya cewa su shagali ne kawai ba za su yi ba, amma za su tsira da kwabbonsu tun da ba za su kashe makuden kudade yadda aka saba ba wajen shagulgulan biki.
Amma ga masu wuraren shirya tarukan biki lamarin ba haka yake ba, tun da su sana'a ce suke yi mai kawo riba, idan ba ciniki kuma sai faduwa.
Hajiya Afiyah Dalhatu, ita ce mai gagarumin wajen gudanar da shagalin bukukuwa da ake kira Afficent a Kano, kuma ta shaida min cewa dole su bi matakin da gwamnati ta dauka da kuma kokarin kare lafiyar mutane duk kuwa da cewa hakan ba karamin shafar tattalin arzikinsu yake ba.
''Kudi ba sa shiga a yanzu sai dai ma su fita. Ina da ma'aikata na dindindin fiye da 100, ban da wadanda mukan kira su yi mana aiki lokaci-lokaci.
''Ma'aikatan dindindin dinnan duk wata muke biyansu. To ban san har zuwa yaushe wannan abu zai ci gaba ba, amma idan abun ya yi nisa da yawa, dole mu hakura mu ba su hakuri,'' in ji Hajiya Afiyah.
Ta kara da cewa: ''Amma wasu kungiyoyi masu zaman kansu na ta kira da a tallafa a hada kayan abinci don rabawa masu karamin karfi idan har aka wayi gari an hana zirga-zirga a Kano.
''To ni na ce musu idan hakan ta kasance gara na ci gaba da taimakawa ma'aikatana a matsayin tawa sadakar tun da idan ma taimako ne an fi su ka fara da na kusa da kai.
Akalla duk mako irin wadannan wurare na yin shagalin biki kan samu masu kama wajen sau uku, daga ranakun Alhamis zuwa Lahadi, sai dai a watan ramadan ne akwai ba a samu.
Hakan kenan na nufin kasuwarsu za ta samu cikas, kamar dai yadda Hajiya Afiyah ta ce: ''Ya yi mummunan tasiri a kan tattalin arzikinmu.
''Cikin abin da muke samu ne muke cire albashi da kudin wuta da man janareto da sauran abubuwa da aywa, to lokuta da dama ma ribar ba ta wuce kashi 10 cikin 100 na abin da ake kashewa.
''Ba wani abu aka tara da yawa da za a ce za a dogara da shi ba a wannan yanayi, ashe kenan idan har aka ci gaba da tafiya a haka nan da wani dan lokaci da yawan masu irin sana'armu za su karye.''
A cikin wannan tsaka mai wuyar aka yi auren diyar Hajiya Afiyah, sai dai duk da cewa ta mallaki katafaren wajen gudanar da liyafa, haka ta hakura don bin matakan kariy aka yi bikin salin-alin.
''Gaskiya duk da cewa na shirya yin biki sosai tare da gayyatar mutane, amma kawai sai na yanke shawarar bin matakan kariya daga yaduwar wannan annoba, aka daura aure aka kai amarya kawai.
''Saboda ina da mutane da dama da suka dawo daga kasashen ketare, don me zan yi taron da za a yi wasa da lafiyar mutane? Ai rashin yin hidimar biki ba ya nufin rashin albarkar aure. Muna fata komai ya warwre a ci gaba da rayuwa yadda aka saba,'' in ji ta.