Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Covid-19: Babu tabbacin gudanar da aikin Hajjin bana — Saudiyya
Saudiyya ta nemi kasashen duniya su dakatar da karbar kudaden jama'a domin zuwa aikin Hajjin bana, a yayin da annobar coronavirus ke ci gaba da mamaye duniya.
Ministan aikin Hajji Mohammed Banten ya ce Saudiyya ta damu da kiwon lafiyar Mahajjata sannan ya yi kira ga jama'a su "jira kafin su biya kudin" aikin Hajji.
Ana sa ran fiye da Mahajjata miliyan biyu ne za su tafi Makkah da Madina a watan Yuli zuwa Agusta domin gudanar da aikin Hajji.
Dole ne dukkan Musulmin da ke da lafiya da halin zuwa ya yi aikin Hajji akalla sau daya a rayuwarsa.
Tuni dai mahukuntan Saudiyya suka dakatar da zuwa Umra, a yunkurinsu na hana yaduwar coronavirus.
An hana mutane shiga Makkah da Madina, da ma babban birnin kasar Riyadh, a kokarin da hukumomin Saudiyya ke yi na hana yaduwar Covid-19, wadda ta harbi akalla mutum 1,563 sannan mutum 10 suka mutu a kasar.
Mr Banten ya shaida wa wani gidan talbijin cewa: "A shirye Saudiyya take ta biya bukatun masu zuwa Hajji da Umra a ko wanne hali.
"Amma a halin da ake ciki, a yayin da muke magana a kan annobar da ta addabi duniya, wacce muke addu'ar Allah Ya kare mu daga gare ta, masarautar Saudiyya ta fi mayar da hankali kan yadda za ta kare lafiyar Musulmi da 'yan kasa."
"Don haka mun yi kira ga 'yan uwanmu Musulmai a dukkan kasashen duniya su jira kada su kammala yarjejeniyar da suke kullawa da kamfanonin jiragen sama har sai komai ya daidaita."
Ya kara da cewa ma'aikatun aikin Hajji da na lafiya sun sanya ido a kan otal-otal da ake amfani da su wajen saukar mutanen da suka je kasar domin yin Umra kafin a dakatar da aiki na Umra kuma aka gaya musu da su killace kansu.
Ministan ya ce za a mayar wa mutanen da aka yi wa bizar Umra amma ba su samu damar gudanar da aikin ba kudadensu.
Karin labarai masu alaka: