Coronavirus: Mutum 65 ne suka kamu da cutar a Najeriya

Lokacin karatu: Minti 1

Hukumar hana yaduwar cutuka ta Najeriya ta ce mutum 65 aka tabbatar sun kamu da coronavirus a kasar.

A sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Alhamis da daddare, hukumar ta yi bayani dalla-dalla game da jihohin da mutanen suka fito kamar haka:

Lagos- 44

Abuja- 12

Ogun- 3

Ekiti- 1

Oyo- 1

Edo- 1

Bauchi-1

Osun-1

Rivers-1

Ta kara da cewa mutm uku sun warke daga cutar sannan mutum daya ya mutu.

Da ma gwamnatin kasar ta nuna matukar rashin jin dadinta game da yadda 'yan kasar suka ki yin biyayya ga umarnin da ta yi musu na daukar matakan kariya a kan cutar.

Ranar Alhamis, ministan watsa labaran kasar, Lai Mohammed, ya ce lokaci yana kurewa Najeriya a yunkurnta na dalike cutar.

Ya koka kan yadda masu cutar suke kin bayyanawa gwamnati gaskiyar hali da suke ciki da halin 'yan kasar na rashin yin tazara a mu'amalarsu da juna da kuma kin yin gwajin cutar.

A cewarsa, dole ne 'yan kasar su bi umarnin gwamnati idan ba haka ba a tursasa musu yin hakan.