Coronavirus: Nigeria na tsaurara matakai kan tafiye-tafiye

Jirgin kasa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hukumar kula da sufurin jirgin kasa ta ce za ta sake fitar da karin bayani

Hukumomi a Najeriya sun bayar da sanarwar dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa a fadin kasar daga ranar Litinin 23 ga watan Maris.

A wata sanarwa da hukumar kula da sufurin jirgin kasa ta fitar, ta ce an dauki wannan matakin ne domin dakile yaduwar cutar ta Covid-19 a kasar.

Sanarwar mai dauke da sa hannun mataimakin babban daraktan hukumar Yakubu musa, ta kara da cewa, za a fitar da karin bayani game da zirga-zirgar jirgin fasinjan da zarar sun samu damar yin hakan.

An samu karin mutum 10 da ke dauke da cutar a ranar Asabar a kasar, kamar yadda ma'akatar Lafiya ta Najeriya ta tabbatar a ranar Asabar. Adadin wadanda ke dauke da cutar yanzu ya 22, biyu sun warke.

Uku daga cikin wadanda suka kamu a Abuja suke, babban birnin kasar, sauran bakwai suna Jihar Legas.

An hana jiragen kasar waje sauka a Najeriya

Jirgin Turkish Airlines

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sai dai jiragen cikin gida za su ci gaba da shiga da fita a filayen jirgin saman

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya NCAA ta sanar da hana jirage daga kasashen waje sauka a dukkanin filayen jirgin saman kasar sakamakon yakin da ake yi na dakile cutar Covid-19.

"Daga ranar 23 ga watan Maris za a rufe wa jirage daga kasashen waje kofa a filayen jirgin sama na Abuja (Nnamdi Azikiwe International Airport) da na Legas (Murtala Muhammed International Airport)," NCAA ta fada a wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar.

Hukumar ta ce wannan kari ne kan filayen jirgin sama na Kano da na Fatakwal da na Akwa Ibom da aka rufe su ranar Asabar. Sai dai ta ce ban da jirage masu saukar gaggawa.

Kazalika, jiragen cikin gida za su ci gaba da shiga da fita a filayen jiragen.