Ganin arha ne zargin Buhari da sakaci kan coronavirus - Gwamnatin Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Fadar shugaban Najeriya ta ce ganin arha ne da zuzuta abu, suka sa wasu mutane ciki har da 'yan majalisar kasar, shiga yekuwar neman suna a wajen talakawa kan batun Covid-19.
Ta ce wannan, ba lokaci ne na neman shiga a wajen talakawa da siyasar ganin arha ba.
Sanarwar da fadar shugaban Najeriyar ta fitar da yammacin jiya na cewa jazaman ne sai duk 'yan kasar Gabas da Yamma, Kudu da Arewa su hada kai a yaki da wannan annoba, ba tare da la'akari da bambancin addini ko akida ba.
A baya-bayan nan Shugaba Muhammadu Buhari na shan suka kan yadda ake zargin ya yi biris ya ki fitowa ya yi wa 'yan kasar jawabi kan halin da ake ciki game da cutar covid-19

Asalin hoton, Getty Images
'Yan Najeriya da dama musamman a shafukan sada zumunta na ta kira ga Shugaba Buhari ya gabatar da jawabi kamar yadda takwarorinsa a fadin duniya suke yi a kokarinsu na shawo kan coronavirus.
Hatta 'yan majalisar dattijan kasar sun fito sun bukaci shugaban Najeriya ya yi wa 'yan kasar jawabi kan batun.
Sai dai fadar shugaban kasar ta ce: "Muna kuma yin kira ga 'yan Najeriya kada su dubi wannan hali da aka shiga a matsayin wata damar nuna siyasa ko amayar da kullatar da suke da shi ga gwamnati ko kuma jam'iyyar APC mai mulki."
Shugaba Muhammadu Buhari ya yaba wa duk jami'an da ke kan gaba-gaba a yakin da Najeriya ke yi da mummunar cutar coronavirus da ta addabi duniya.


Fadar shugaban ta ce suna da babban kwamitin hadin gwiwa na shugaban kasa karkashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Tarayya. Kuma a cewarta an bai wa kwamitin damar gudanar da duk wasu nauye-nauye kan wannan lamari.

Asalin hoton, @NGRPresident
Don haka suka bukaci goyon bayan dukkanin dan Najeriya ya yi aiki tare da gwamnati a yaki da cutar covid-19 kuma a bi duk wani umarni daga Cibiyar takaita yaduwar cutuka ta Najeriya.

Ba ma son firgita jama'a
Fadar shugaban Najeriya ta ce ba ta son tayar da hankula, amma dai za su ci gaba da fitar da sabbin bayanai masu fa'ida ga 'yan kasar.
Ta ce daga cikin matakan da hukumomi ke dauka don yaki da cutar coronavirus har da sanarwar da Babban Bankin Najeriya ya fitar a ranar Litinin ta samar da rancen naira tirliyan 1 da biliyan 100 ga harkokin kasuwancin da wannan annoba ta shafa.
Haka zalika, bankin ya samar da wani asusun ba da tallafi ga magidanta da masu kanana da matsakaitan sana'o'i da kuma sanar da rage kudin ruwa a kan basuka daga kashi 9% zuwa kashi 5%
Haka shi ma, Kamfanin samar da man fetur na kasar NNPC ya sanar da ragin naira 20 a kan litar man fetur guda, daga naira 145 zuwa naira 125 a yanzu.
"Annobar Covid-19 ta janyo faduwar farashin danyen man fetur a duniya, don haka shugaban kasa ya ce su ma 'yan Najeriya, ya kamata su ci moriyar wannan ragi da aka samu" in ji sanarwa.
Ta ce Shugaba Buhari ya aminta da ministocin da ke da jibi a majalisar ministocinsa da kuma jami'an Cibiyar Takaita Yaduwar Cutuka ta Najeriya, wadanda ke ba shi sabbin bayanai da shawarwarin kwararru.
A cewarta "Wadannan jami'ai daga abin da ya bayyana game da ayyukansu suna da kwarewa. Fadar shugaban kasa na son tabbatar wa 'yan Najeriya cewa lamarin bai fi karfin gwamnati ba."
Ta ce babu bukatar kowa ya firgita. Zuwa yanzu matakan da aka dauka suna aiki da inganci.
A yanzu haka akwai kwararan matakan bincike da ake dauka a hanyoyin shiga Najeriya na sama da na teku, in ji ta.
Kuma duk kokarin da Najeriya ke yi a bayyana yake, tun da har "Hukumar Lafiya ta Duniya ta fito ta yaba mana".
Hukumomin gwamnati daban-daban ciki har da kafofin yada labarai sun fara gagarumin wayar da kai kan matakan inganta tsafta.
Haka zalika, don kare bazuwar kwayar cutar zuwa Najeriya, shugaban kasa a cewar sanarwar tuni ya ba da umarnin sanya tarnakin shigo wa kasar a kan kasashe 13, da aka samu yawan masu fama da coronavirus.
Ta ce ko da yake Najeriya tana murnar marabtar baki daga fadin duniya, amma kare lafiya da tsaron 'yan kasa da ma kasar kanta ne abubuwan da suke bai wa fifiko.
A cewarta wannan haramci na shiga kasar daga wadancan kasashe guda 13 zai ci gaba da kasancewa daga ranar 20 ga watan Maris har sai an ji sanarwa ta gaba a kan batun.











