Coronavirus: Me ya sa Buhari ya yi gum da bakinsa?

Buhari

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Fadar shugaban Najeriya ta ce Shugaba Muhammadu Buhari ya ki yi wa 'yan kasar jawabi game da cutar Coronavirus ne saboda ya dora alhakin yin jawabi ga jami'an kiwon lafiya da na gwamnatin kasar.

Kakakin shugaban kasar Malam Garba Shehu, wanda ya shaida wa BBC hakan a hirar da muka yi da shi, ya kara da cewa yawan zuzuta batun zai tayar da hankalin 'yan Najeriya.

Ranar Alhamis aka samu sabbin mutum hudu da suka kamu da Coronavirus a jihar Legas, inda adadin mutanen da suka harbu da cutar ya kai 12.

Shugabannin kasashe da dama suna yi wa 'yan kasarsu jawabi a kan halin da kasashensu ke ciki game da cutar.

Hasalima, Shugaba Muhammad Issoufou na Jamhuriyar Nijar, inda ba a samu ko da mutum daya da ya kamu da cutar ba, ya yi wa 'yan kasar jawabi kan matakan da gwamnatinsa ke dauka domin yin riga-kafin cutar.

'Yan Najeriya da dama musamman a shafukan sada zumunta na kira ga Shugaba Buhari ya yi wa kasar jawabi game da matakin da gwamnatinsa ke dauka wurin shawo kan cutar ta Coronavirus.

Kazalika, 'yan majalisar dattawan kasar sun bukaci shugaban Najeriya ya yi wa 'yan kasar jawabi kan batun.

Sai dai Malam Garba Shehu ya ce ko da yake akwai bukatar Shugaba Buhari ya yi jawabi, amma bayanan da jami'an gwamnati irin sa ke yi sun wadatar.

"Mu din nan da su ministan lafiya ai duk 'yan aikensa ne; idan muka yi kalamai a madadinsa ai ya gamsar tun da ba za mu fada ba sai ya ce a fada."

Malam Garba Shehu ya ce bai kamata a rika zuzuta irin wannan batu ba domin yana iya tayar da hankalin 'yan kasar.

Kakakin shuugaban kasar ya ce gwamnati ta ware fiye da naira biliyan daya domin yaki da Coronavirus, yana mai cewa an kafa kwamiti na musamman wanda sakataren gwamnatin tarayya ke jagoranta domin sanya ido kan batun na Coronavirus.

Mun yi wannan hira ne da Malam Garba Shehu kafin a samu sabbin alkaluman mutanen da suka kamu da coronavirus a Najeriya.

Mun so jin karin bayani a wurinsa game da ko gwamnati ta sauya matsayinta kan jawabin da 'yan Najeriya ke son Shugaba Buhari ya yi musu, amma mun ta kiran wayarsa sai dai bai dauka ba.