Kotu ta nemi a mika sojojin da suka saki Wadume

Asalin hoton, Twitter/@PoliceNG
Wata kotu a Najeriya ta umarci rundunar sojin kasar ta mika sojojin da ake zargin suna da hannu wajen kubutar da Hamisu Bala, wanda ake wa lakabi da Wadume, bayan 'yan sanda sun kama shi.
A watan Agustan da ya wuce 'yan sanda suka kama shi a jihar Taraba da ke arewacin kasar bayan da suka yi zarginsa da hannu wajen satar mutane domin karbar kudin fansa.
Sai dai a wancan lokacin rundunar 'yan sandan ta zargi wasu sojojin kasar da hallaka jami'anta uku tare da raunata wasu bayan da sojojin suka bude wuta kan tawagar 'yan sandan da ta kamo Wadume.
Babbar kotun tarayyar, wadda mai shari'a Binta Nyako ke jagoranta, ta umurci manyan jami'an soji, wato da babban hafsan hafsoshin sojin Najeriya, Abayomi Olonisakin, da kuma hafsan sojojin kasa na kasar, Yusuf Tukur Buratai su gabatar da sojojin da ake zargi suna da hannu a sakin Hamisu Wadume.
Lauya mai gabatar da kara, Simon Lough ne ya bukaci kotun da ta tilasta wa manyan jami'an sojin da su yi hakan domin wadanda ake zargin su fiuskanci shari'a.
Kotun dai ba ta saurari bahasi daga Hamisu Bala Wadume da sauran wadanda ake tuhuma ba, kasancewar sojojin da ake zargin ba su bayyana a kotun ba.
A ranar 6 ga watan Agustan da ya wuce ne wani ayarin rundunar 'yan sanda ta musamman da ke yaki da masu satar mutane da 'yan fashi ta yi artabu da wasu sojoji a jihar Taraba da arewa maso gabashi Najeriya.
Hakan ya faru ne lokacin da 'yan sandan, dauke da hamisu Wadume cikin sarka suka ta samma wani shinge da sojojin suka kafa, inda sojojin suka bude musu wata, har wasu daga cikin 'yan sandan suka riga mu gidan gaskiya.
Rahotanni dai sun Ambato sojojin suna cewa agajinsu aka nema da su ceci Wadume kasancewar wasu masu satar mutane ne suka sace shi, yayin da wasu rahotannin ke cewa hedikwatar 'yan sanda da ke jihar Taraba ma ba ta da labarin zuwan 'yan sandan.
Amma daga bisani 'yan sandan sun musanta.
Yanzu dai mai shari'a Binta Nyako ta dage zaman kotun zuwa 30 ga wannan wata na Maris don ci gaba da shari'ar.











