Babu adalci kan mutum 640 da sojojin Najeriya suka kashe – Amnesty

Asalin hoton, Amnesty International
Kungiyar kare hakki ta Amnesty International ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta yi adalci wajen bincike dangane da zargin da ake yi wa sojojin kasar na kashe mutum 640 a Barikin Soja na Giwa da ke Maiduguri.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta wallafa a shafinta na Twitter cewa iyalan wadanda aka kashe na bukatar gwamnati ta yi musu adalci ta yi bincike dangane da wannan lamari da ya faru shekaru shida da suka gabata.
A watan Maris din 2014 ne dai aka bayar da rahoton cewa wasu karin sojojin Najeriya sun garzaya barikin sojoji na Giwa wanda aka fi sani da Giwa Barracks da ke Maiduguri domin dakile wani hari da 'yan Boko Haram suka kai.
A lokacin, an zargi sojojin da kashe wasu fursunonin da ake zargi 'yan Boko Haram ne 640.
Barikin sojin na Giwa wuri ne da ya yi suna wajen tsare wadanda ake zargi da hannu a kungiyar Boko Haram.
Kungiyar Amnesty International dai ta sake kokawa da rashin adalcin ne yayin da ake cika shekaru shida da faruwar lamarin
An bayyana cewa karin sojoji sun garzaya barikin sa'o'i kadan bayan 'yan kungiyar Boko Haram sun shiga sansanin sun ceto daruruwan mambobinsu da ke tsare.
Sai dai wadanda ake zargin sojojin sun kashe bayan sun shiga barikin sun hada da wasu da ake zargin ragowar 'yan Boko Haram ne wadanda ba a samu tserewa da su ba da kuma kananan yara wandanda ake zargin sojojin da raunata.
Bayan irin wutar da aka huro wa rundunar sojin kasar a sheakrun baya kan wannan zargi, rundunar ta ce ta kafa kwamiti na bincike domin gano musabbabin abin da ya faru, sai dai shekaru shida kenan babu wasu kwararan hujjoji da rundunar ta bayar.
A wannan karon ma, ko da BBC ta tuntubi mai magana da yawun sojojin Najeriya Kanal Sagir Musa, ya shaida mana cewa shi kansa bai san inda aka kwana ba kan wannan batu ba domin lokacin da abin ya faru a 2014, ba shi Najeriya yana Ingila, amma zai gudanar da bincike ya tuntube mu da karin bayani.
Gwamnatin Najeriya dai ta dade tana ikirarin karya lagon kungiyar Boko Haram da ta addabi yankin arewa maso gabas, amma har yanzu mayakan kungiyar na ci gaba da yi wa mutanen yankin barazana.











