Yadda aka yi da kadarorin Muhammadu Sanusi na II da ke Fadar Kano

Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II

Asalin hoton, Kano Emirate

Bayanan hoto, Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II na son kawa, tun daga motocin alfarmarsa da dakin karatunsa da kuma manyan riguna

A yayin da sabon sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya shiga Fadar Masarautar, makusantan Muhammad Sanusi na II sun ce sun kwashe littattafan tsohon sarkin fiye da 42,000 da kudinsu ya kai kimanin naira milliyan 200.

Falakin Kano Mai Murabus Mujitaba Abubakar Abba wanda shi ne tsohon babban sakatare na fadar sarkin ne ya bayyana hakan a wata hira da yayi da BBC yace dan uwan nasa, Muhammad Sanusi ya bar daukacin dawakan sa da sauran kayan daki da aka zuba na kawa a gidan sarkin domin amfanin wanda ya gajeshi, sannan sun dauke motocin da suke mallakin toshon sarkin na Kano.

An fara kwashe kayan tsohon sarkin na Kano Muhammad Sanusi tun bayan da aka dauke shi daga fada kuma an kammala kwashe kayan a ranar Laraba, kafin sabon sarkin Aminu Ado Bayero ya shiga gidan bayan Sallar Magariba.

Duk wanda yake mu'amala da shafukan sada zumunta ya san irin yadda tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ke son kawa, tun daga motocin alfarmarsa da dakin karatunsa da kuma manyan riguna.

Falakin Kano Mai Murabus Mujitaba Abubakar Abba, ya shaida wa BBC cewa mai martaba ya fi damuwa da litattafansa sama da komai bayan ya bar gidan sarautar a ranar Talata.

"Ka san shi da harkar littattafai, saboda haka su ne muka mayar da hankali wurin kwashewa domin killace su," in ji Mujitaba Abubakar Abba.

Ya kara da cewa Muhammadu Sanusi II ya so a bar su a masararutar idan har akwai tabbas cewa sabon sarki zai yi amfani da su.

Kadarorin Muhammadu Sanusi II

Dakin karatun Mai Martaba guda uku ne, in ji Falakin Kano mai murabus - na sama da na kasa da kuma tsohon dakin karatun - kuma akalla akwai littafi 42,000 a cikinsu.

Sarki Sanusi

Asalin hoton, Kano Emirate

Bayanan hoto, Muna da kididdiga tsakanin littafi da mujalla mai martaba yana da akalla 40,000 da doriya, ban da kuma wadanda suke kan hanya daga Ingila zuwa Legas kusan 22,000,"in ji Mujitaba Abubakar

"Muna da kididdiga tsakanin littafi da mujalla mai martaba yana da akalla 40,000 da doriya, ban da kuma wadanda suke kan hanya daga Ingila zuwa Legas kusan 22,000," in ji Mujitaba Abubakar.

"Amma yanzu wadanda muka dauka daga gidan sarki sun kai akalla 42,000.

"A takaice dai litattafan nan ba su gaza naira miliyan 200 ba - wannan abin da nake iya sani kenan - domijn kuwa akwai wadanda yake da su tun yana makaranta."

Motoci

"Ina iya tunawa, lokacin da sarki zai fita ya ce da wanda zai gaje shi zai yi amfani da wadannan kayan da shi ba zai taba ba, da sai ya bar masa domin ya yi amfani da su," Falakin Kano mai murabus ya ce.

Falaki ya ce sha'anin sauyi abu ne daban, saboda haka sun dauke motocin sarki kuma sun killace su.

Saurari cikakkiyar hirar tahanyar latsa hoton da ke kasa:

Bayanan sautiMuryar Falakin Kano

Tufafi

Falaki Mujitaba ya ce sun samu damar tattare kayan sakawar mai martaba su ma.

A cewarsa, "komai na iya faruwa a dan tsakanin nan, saboda ka da masu shigar da kaya (su taba) kuma ba a bai wa masu bukata ba kuma shi wanda zai shigo din bai amfana ba".

Ya ce sun killace wasu daga cikin alkyabbunsa da takalmansa da ma rigunansa.

littattafan Sarki Sanusi

Asalin hoton, Kano Emirate

Dawakai da sirada

Sarki Sanusi mai murabus ya bar wa wanda zai gaje shi dawakansa da siradansa baki daya domin ya yi amfani da su, in ji Falakin Kano mai murabus Mujitaba Abubakar Abba.

"Sirdi guda daya kadai ya ce a daukar masa. Shi kuma wannan sirdi mai tarihi - ya gaje shi ne daga Ciroman Kano (mahaifnsa), shi kuma Ciroma ya gaje shi daga Sarki Halifa, Sarki Halifa ya gaje shi daga Sarki Abdullahi Bayero, shi kuma ya gaje shi daga Sarki Abbas."

Mujitaba Abubakar ya kara da cewa "sai kuma takobinsa guda daya ita ma mai dumbin tarihi".

Sarki bai ce a taba duk wani abin da yake a Dogon Gida ba da soro - irin su kujeru da sauransu, kuma a sanin Falaki mai murabus, ba a taba su ba.