An bukaci Najeriya ta rage darajar naira

Asalin hoton, Getty Images
Bankin JPMorgan ya bukaci Najeriya ta rage darajar Naira da kashi 10 cikin dari nan da karshen watan Yuni bayan faduwar farashin man fetur, a cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Reuters ya tuntubi Babban Bankin Najeriya na CBN amma bai mayar da martani ba.
Sai dai CBN ya yi hasashen wasu matakai da suka fi na rage darajar naira girma idan har farashin man ya rikito daga dala 40 ko 30.
A lokacin da farashin mai ya fadi a shekarar 2014, Najeriya ta kare darajar naira ta hanyar dakile zirga-zirgar kudaden kasashen waje, maimakon rage darajar kudin kasar.
Jami'in bankin JPMorgan, Ayomide Mejabi, ya ce a wannan karon yana tsammanin CBN ya rage darajar naira da kashi 10 zuwa naira 400 a kan dala daya, ba kamar yadda take a yanzu ba na 366.3 a kan dala daya.
Najeriya na daya daga cikin kasashe masu tasowa da suke kayyade darajar kudinsu, inda take tsara yadda dala za ta shiga ta fita daga kasar da kuma ajiyar kudin CBN.
Sauran kasashe irinsu Angola da Venezuela sun saukaka matakansu domin bai wa takardun kudaden kasarsu damar yi wa kansu matsayi a kasuwa canjin kudi.
Jami'in bankin JPMorgan, Ayomide Mejabi ya ce yana tsammanin CBN ba zai maimaita abin da y yi ba a shekarun 2014-2016, lokacin da aka samu faduwar farashin man.
"Muna ganin CBN ba zai maimaita kuskuren da ya yi ba a rikicin 2014-2017 lokacin da ya toshe hada-hadar kudaden kasashen waje ta hanyar kayyade darajar naira," in ji shi.
Ya kara da cewa suna sa ran wannan karon bankin zai kyale kasuwar canjin kudaden kasashen waje ba tare da an dabaibaye ta da dokoki ba.











