Hukumar yaki da rashawa za ta ci gaba da binciken Sarki Sanusi II

Bayanan sautiZa a ci gaba da binciken Sarki Sanusi II

Ku latsa alamar lasifika a hoton da ke sama domin sauraren hira da Muhuyi Magaji:

Hukumar yaki da rashawa da cin hanci ta jihar Kano a Najeriya ta ce za ta ci gaba da gudanar da bincike kan Sarki Muhammadu Sanusi II bisa zargin badakalar sayar da filaye mallakar masarautar Kano.

Shugaban hukumar Muhuyi Magaji ya shaida wa BBC cewa cire Sarki Sanusi II daga sarauta zai ba su damar fadada binciken da suke yi a kansa.

"Ina so mutane su fahimta cewa abin da muke yi a hukumarmu yana da bambanci da abin da ake yi a gwamnati. Wancan [cire Sarki daga kan mulki] abin da gwamnati suke yi mataki ne na mulki. Mu kuma abin da muke yi ya shafi laifuka ne. Saboda haka bincike yana nan, kuma ina ganin wannan wata dama ce da gwamnati ta ba mu ta yin bincike," in ji Muhuyi.

A watan jiya ne wata kotun tarayya ta soke rahoton da hukumar yaki da rashawar ta Kano ta fitar wanda ya nemi gwamnatin jihar ta dakatar da Sarki Sanusi II.

Kotun ta kuma umarci hukumar ta biya Sarkin Naira 200,000 a matsayin kudin shari'ar da ya kashe.

Sai dai a wancan lokacin, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ce za ta ci gaba da binciken Sarkin.

Muhyi Magaji

Asalin hoton, Muhuyi Magaji Rimingado

Bayanan hoto, Muhuyi Magaji ya ce cire Sarki Sanusi II zai ba su damar fadada bincike a kansa

A baya dai hukumar ta kama wasu ma'aikatan fadar sarkin Kano inda ta zarge su da laifin karbar rashawa kan wani wani fili da suka sayar a unguwar Hotoron Arewa da ke birnin Kano kan naira miliyan 80.

Ita ma majalisar dokokin jihar tana gudanar da bincike kan Sarkin bisa zarginsa da yin wasu abubuwa da ska saba da addini da al'adun jihar ta Kano.