Manyan 'yan Republican sun kebe kansu saboda coronavirus

Asalin hoton, EPA
Manyan 'yan jam'iyyar Republican biyar sun kebe kansu bayan da suka kusanci wani mutum da aka tabbatar ya kamu da coronavirus.
'Yan majalisar har da Sanata Ted Cruz sun killace kansu bayan sun yi musabaha da mutumin da ya kamu da cutar a wani taro.
Shugaba Donald Trump wanda ya halarci taron a watan da ya gabata, ya dage cewa ya na cikin koshin lafiya kuma ba a yi masa gwaji ba.
Wata 'yar Demokrat ita ma ta killace kanta bayan ta hadu da wani mai dauke da cutar.
Akwai sama da mutum 700 da suka kamu da cutar a Amurka - mutum 26 kuma sun mutu kawo yanzu.
Mista Cruz da Paul Gosar da Doug Collins da Matt Gaetz duk sun kebe kansu na tsawon mako biyu bayan da suka gana da wani da ya kamu da coronavirus a wani taron siyasa a karshen watan Fabrairu.
Dan majalisa na jam'iyyar Republican Mark Meadows wanda Shugaba Donald Trump ya nada a matsayin shugaban ma'aikata shi ma ya hadu da mutumin kuma ya killace kansa.
Bai nuna alamun kamuwa da cutar ba sannan gwajin da aka yi masa ya nuna ba ya dauke da cutar, a cewar wani mai magana da yawunsa.











