Coronavirus: WHO ta yaba aikin Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban WHO ya ce "Najeriya na yunkuri mai amfanin gaske wurin dakile yaduwar coronavirus
Lokacin karatu: Minti 2

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ya yaba da yadda Najeriya ke aikin dakile annobar cutar nimfashi ta coronavirus.

Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter biyo bayan rahoton da hukumar kiyaye yaduwar cutuka ta Najeriya ta wallafa irinsa na farko a kasar kan yaduwar kwayar cutar.

"Muna godiya ga hukumar NCDC da gwamnatin Najeriya kan yadda suka zayyana yaduwar cutar COVID19 a kasar," Tedros Adhanom ya fada.

Ya kara da cewa "wannan shi ne aiki karara na bayar da hadin kai kuma mai amfanin gaske wurin dakile coronavirus daga ci gaba da yaduwa".

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Najeriya ta tabbatar da rahoton bullar cutar coronavirus ranar 27 ga watan Fabarairun 2020 a asibitin Yaba da ke Legas.

A sanarwar da ya fitar, Ministan Lafiya na Najeriya, Dr Osagie Ehanire, ya ce wani dan kasar Italiya ne da ke aiki a kasar ya shigo da cutar bayan ya dawo Lagos daga birnin Milan.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Hanyoyi 4 na kare kai daga coronavirus

■ Ku wanke hannayenku da sabulun gargajiya ko sabulun ruwa da ake wanke hannu da shi, wato hand gel, wanda zai iya kashe kwayoyin cuta

■ Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da kyallen fyace majina - sannan ku wanke hannayenku bayan kun yi atishawa domin hana kwayoyin cutar yaduwa.

■ Ku guji taba idanunku, ko hanci ko bakinku- idan hannunku ya taba wurin da cutar ta shafa, za ta iya yaduwa zuwa sauran sassan jikinku.

■ Kada ku rika matsawa kusa da mutanen da ke yawan atishawa ko tari da masu fama da zazzabi - za su iya watsa cutar cikin iska ta yadda ku ma za ku iya kamuwa da ita. - akalla ku matsa nesa da su ta yadda tazarar da ke tsakanin ku za ta kai kafa uku.