Mutanen gari sun kashe 'yan bindiga 17 a Katsina

Aminu Bello Masari

Asalin hoton, Twitter

Bayanan hoto, Maharan sun kashe 'yan garin guda hudu

Rundunar 'yan sanda a jihar Katsina da ke Arewa maso yammacin Najeriya ta ce ta karfafa matakan tsaro a garin Gurbi da ke karamar hukumar Kankara, bayan 'yan fashin daji sun afkawa wa garin.

An yi dauki ba dadi tsakanin 'yan bindigar da mutanen garin, inda 'yan garin suka kashe 17 daga cikin 'yan bindigar, in ji rundunar 'yan sandan jihar.

Maharan sun kashe 'yan garin guda hudu yayin da rahotanni ke cewa tsoron harin ramuwa ta sa mazauna tserewa domin tsira.

A daren Alhamis ne 'yan bindiga suka afka wa garin bayan "sun sato dabbobi" daga wasu kauyuka da nufin karawa da wasu a garin kafin su wuce, a cewar rahotanni.

Mutanen garin sun yi wa 'yan bindigar tirjiya inda suka fafata da su har suka kashe da dama daga cikin 'yan bindigar.

Gaskiya an mutu sosai. Ni a gani na, mutum 17 tabbas na ga gawar kowanne daga cikin 'yan bindigar da aka kashe, in ji wani mazaunin garin mai suna Isah Adamu.

Ya kara da ce mutane sun yi artabu da 'yan gari a kauyukan Gidan Alhaji Audu da Katantu da Majifa da Farin Dutse da kuma sassan garin Gurbi.

Malam Isah ya ce rade-radi da fargabar 'yan fashi na iya kawo harin ramuwar gayya ta sa mata da kananan yara yin kaura daga garin.

''Daga Gurbi zuwa kewaye tsakani da Allah, mazaje ne kawai suka rage. Mata daidaiku ne kawai. Har yanzu a bakin tasha ga mata nan masu jiran mota, wasu ma ba su san inda za su ba.''

Kakakin rundunar 'yan sanda jihar Katsina SP Gambo Isah ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce tun cikin daren jiya, bayan da suka samu kira daga garin na Gurbi, ya ce suka aika jami'an tsaro.

Ya kuma tabbatar da kwato dabbobi da suka hada da shanu da tumaki 80 da 'yan fashin suka sace a kauyukan.