Yadda 'yan bindiga suka kashe mutum 30 a Katsina

Tashin hankali a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Wasu 'yan bindiga sun kai hari a garuruwa biyu na yankin karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina da ke arewacin Najeriya.

Ganau sun shaida wa BBC cewa 'yan bindigar sun hallaka mutane da dama kuma sun banka wa gidaje wuta a kauyukan Dankar da Tsanwa.

SP Gambo Isa, jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, ya tabbatar wa BBC faruwar lamarin yana mai cewa an kai hare-haren ne da yammacin Juma'ar da ta gabata amma ya ce rundunarsa ta tura jami'an tsaro yankin.

Da yawa daga mutanen wadannan garuruwan sun tsere sun bar yankin kuma suna gudun hijira a wasu kauyukan.

Wani ganau da ba ya so a bayyana sunansa ya shaida wa BBC cewa ranar Juma'a "bayan sallar Juma'a can da yamma wajen karfe shida da rabi mutane a kan mashin da yawansu suka zo suka kewaye garin suan ta harbi.

"Da kyar na sha na buya a wajen wani dutse amma ko a nan ma an kashe mutum uku," in ji shi.

Ya ce sai da gari ya waye sannan suka samu damar fitowa domin duba halin da garin nasu yake ciki, "cikin garin Dankar abin da na gani mutum takwas aka kashe."

Ya bayyana cewa a garin Tsanwa inda a nan ne aka fi kashe mutane ya ga gawa 27 kuma wasu daga cikinsu duk an kona su.

A cewarsa, baya ga bil Adama da aka kashe a garuruwan biyu, maharan sun kona gidaje da dabbobi kuma sun yi awon gaba da babura da sauran dukiyoyin mutane.

Aminu Bello Masari

Asalin hoton, Facebook

Bayanan hoto, Ana ci gaba da kai hare-hare duk da sulhun da gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, ya yi da 'yan bindiga

Har asibiti aka kai hari

Wani ganau na daban, ya bayyana wa BBC cewa maharan basu kyale marasa lafiya da ke kwance a asibiti ba don kuwa sun je har wani asibiti a Dankar sun harbe masu jinya.

"Akwai wani mara lafiya da ya tsere ta taga, ya nufi hanyar makabarta domin ya buya amma suka bi shi can suka kashe shi," in ji shi.

Ya ce a garin Tsanwa, wasu kiri da muzu maharan suka kona su a cikin gidajensu suka hana su guduwa.

SP Gambo ya ce gaba daya mutane akalla talatin ne suka mutu a tagwayen hare-haren.

Ya kuma ce a garin Dankar an kashe daya daga cikin maharan har ma an kwace bindiga daya daga hannunsa.

"A garin Tsanwa ma an buge babur din wani daga cikin 'yan ta'addar" a cewar SP Gambo amma bai ce an kama shi ba ko a'a.

Ya ce suna bincike kan wani mutum guda da suka kama dangane da hare-haren.

Tuni fadar gwamnatin Najeriya ta fitar da sanarwar jaje da yin Allah wadai da wadannan hare-hare da aka kai.

A watan Janairun wannan shekarar ne gwamnatin jihar ta Katsina ta kafa dokar hana amfani da babura masu kafa biyu da masu kafa uku da aka fi sani da Napep, a fadin jihar a wani mataki na kare rayukan al'umma.

Gwamnatin ta ce babban makasudin kafa dokar shi ne yaki da barayi da masu garkuwa da mutane da suke amfani da babur din wajen tafka ta'asa.

Sai dai da alama wannan doka ba ta hana barayi da 'yan bindiga gudanar da ayyukansu ba a jihar.

Lamarin tsaro a jihar Katsina dai ya jima da shiga halin ha'ula'i, kamar makwabciyarta Zamfara, inda 'yan bindiga ke ayyukan satar mutane da dabbobi da kashe mutanen.

Jihar na cikin jihohin da suka cimma sulhu da `yan bindiga, amma harin da ake kaiwa a baya-bayan nan na nuna cewa sulhun na fuskantar barazana.