'Yan bindiga sun hana mu sakat a kauyukan Katsina'

Bayanan sautiWani dan jihar Katsina

Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraron hirar Sulaiman Katsina da mazaunin wani kauye a Katsina.

A yayin da hukumomi a jihar Katsina ke bugun kirji cewa yarjejeniyar da suka kulla da 'yan bindiga na aiki, wasu mazauna kauyuka a jihar sun ce har yanzu babu zaman lafiya.

A hira da Sulaimanu Ibrahim Katsina, wani mazaunin wani kauye a jihar ta Katsina da ya nemi a boye sunansa saboda dalilan tsaro, ya shaida wa BBC cewa a yanzu wata matsala da suka fuskanta ita ce yadda 'yan bindigar ke zuwa da dabbobinsu cikin gonaki su cinye musu amfanin gona.

Wannan dai na zuwa ne mako daya bayan da gwamnan jihar ta Katsina, Aminu Bello Masari ya jaddada cewa shirin sasanci da 'yan bindiga domin samun tsagaita wuta na aiki dari bisa dari a jihar.

Gwamna Masari ya kara da cewa "wasu 'yan sumoga ne gayyatar 'yan bindigar domin su yi garkuwa da jami'an kwastam da ma mutanen gari."