Sojojin Saudiyya za su fuskanci shari'a kan yakin Yemen

A Yemeni boy receives treatment at a hospital following a Saudi-led coalition air strike on a bus in Dahyan, Saada province, on 9 August 2018

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A kalla yara 'yan makaranta 29 ne suka mutu a wani hari da rundunar sojin hadakar ta kai ta sama kan wata motar bas a Dahyan a 2018

Rundunar sojin hadaka da saudiya ke jagoranta a Yemen ta ce ta fara sauraron kararraki kan dakarunta da ake zargi da karya dokokin kasa da kasa da ke kare hakkin dan adam.

Mai magana da yawun rundunar Kanar Turki al-Maliki ya ce za a sanar da hukuncin da aka yanke a shari'o'in da ba a bayyana maudu'insu ba da zarar an kammala.

Kwararru na Majalisar Dinkin Duniya MDD sun ce za a iya samun rundunar hadakan da laifukan yaki.

Sun kuma bayyana damuwa a kan 'yancin gashin kai na sashen da rundunar hadakan ta samar don nazarin zarge-zargen karya dokokin.

Yemen ta fara fuskantar yakin basasan da ya ta'azzara ne a watan Maris din 2015, lokacin da 'yan tawayen Houthi suka kwace iko da mafi yawan yammacin kasar suka kuma tursasa wa Shugaba Abdrabbuh Mansour tserewa daga kasar.

Bayan Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa da wasu kasashen Larabawa bakwai suka farga da bunkasar wata kungiya da suka yi amannar Iran na goyawa baya, sai suka fara wata fafutuka da nufin dawo da gwamnatin Mista Hadi.

Majalisar Dinkin Duniya ta tantance mace-macen a kalla fararen hula 7,500, wadanda da yawan su hare-haren sama na rundunar hadakan ne suka yi sanadin su.

Wata kungiya da ke sa ido ta kiyasta cewa yakin ya kashe mutum 100,000, da suka hada da fararen hula 12,000.

A wani taron manema labari a Landan ranar Laraba, Kanar Maliki ya kara tabbatar da shirin rundunar "hadin gwiwar na bin dokokin dan adam na kasa da kasa tare da hukunta dakarun da suka saba ka'idar aikinsu da duk wanda aka samu da karya dokokin kasa da kasa - daidai yadda dokokin kasashen wadanda aka samu da laifi", a cewar kamfanin dillancin labarai na Saudiyya SPA.

Rundunar ta tura wa kasahen da ta shafi dakarunsu "kundayen bayanan sakamakon binciken da aka gudanar kan zarge-zargem domin gano kurakurai ko laifukan da aka aikata ."

Ya kara da cewa hukumomin shari'a sun fara nazarin kan bayanan domin fara sauraron kararrakin.

Harin saman da ya kashe mutum 19 a asibitin kauyen Absa a 2016

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Harin saman da ya kashe mutum 19 a asibitin kauyen Absa a 2016

SPA bai fayyace laifukan da za a bincika ba, amma jaridar Guardian ta ambato cewa sojojin sama za su fuskanci shari'a kan wasu hare-hare guda uku.

  • Harin saman da ya kashe mutum 19 a asibitin kauyen Absa a 2016.
  • Harin sama da aka kashe mutum 20 a wurin bikin daurin aure a Bani Qayis a watan Afrilun 2018.
  • Harin sama da aka kashe akalla mutum 29 a cikin motar safa a yankin Dahyan a watan Agustan 2018.

A watan Satumba ne kwararrun MDD kan Yemen suka ce akwai kwararan hujjojin da ke tabbatar da sojojin rundunar da Saudiyyar da masu goyon bayan gwamnatin Yemen sun aikata laifukan yaki da suka hada da:

  • Kai hare-haren soji a kaikaice, sabanin abin da dokar rarrabe tsakanin mutane ta yi tanadi.
  • Kai hare-haren sama sabanin dokar rarrabewa tsakanin mutane da lura da girman illar da hakan.
  • Kisan kai, azabtarwa, cin zarafi, musgunawa, fyade da cin mutunci ta hanyar kin gurfanarwa a gaban kotu da kuma daukar yara 'yan kasa da shekara 15 aikin soji ko kuma amfani da su a matsayin mayaka.

Rahoton ya kuma zargi 'yan tawayen Houthi da aikata laifukan yaki da suka hada da kai wa fararen hula hari da harbin mai uwa da wabi da aikata kisan kai da azabtarwa da yin garkuwa da mutane da kuma amfani da kananan yara a matsayin mayaka.

Rundunar da Saudiyya ke jagoranta ta dage a kan cea tana bin doka

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Rundunar da Saudiyya ke jagoranta ta dage a kan cea tana bin doka

Kwararrun sun nuna shakku "game da sahihanci da adalci da zurfin bincike da sakamakon da za a samu daga binciken" kwamitin da Saudiyya ta kafa domin gudanar da bincike a kan zarge-zargen saba dokokin.

"Nazarin kwamitin a kan yadda aka kai hare-haren babban abin damuwa ne, domin doka ta halasta kai hari a kan wuraren soji ko da akwai fararen hulaba. Hakan ya nufin an yi watsi da dokar lura da kuma ka'idar rarrabe tsakanin mutane da kuma yawansu", inji kwamitin.

Map of Yemen showing areas of conflict and control (December 2019)
Presentational white space