An kaddamar da manhajar gano hadarin kamuwa da Coronavirus

People wearing protective face masks commute on a train in Shanghai.

Asalin hoton, Getty Images

China ta kaddamar da wata manhaja da take bai wa mutane damar duba ko suna cikin hadarin kamuwa da cutar Coronavirus.

Manhajar tana sanar da masu amfani da ita idan sun kusanci mutumin da aka tabbatar ya kamu da cutar ko kuma ake zargin ya kamu da ita.

Ana neman wadanda suke da hadarin kamuwa da cutar su yi zamansu a gidajensu tare da sanar da hukumomin lafiya.

Wannan manhaja kuma tana haska yadda gwamnatin China take sa ido kan al'ummarta.

Idan mutum ya yi rajista da manhajar ta amfani da lambar waya, manhajar na neman mutum ya rubuta sunansa da kuma lambar tantancewa.

Za kuma a iya amfani da duk lambar wayar da aka yi wa rijista da manhajar wajen duba matsayin lambobin tantancewar har uku.

Wasu sassa na gwamnatin China da kamfanin laturoni na kasar ne suka kirkiri manhajar tare da samun bayanai daga hukumomin lafiya da na sufuri a cewar kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Sanannen abu ne cewa gwamnatin China na sa ido kan jama'ar kasar sai dai kwararru a fannin na ganin manhajar ba za ta haifar da wata takaddama a kasar ba.

Screen grabs of China's new coronavirus 'close contact detector' app.
Bayanan hoto, Ana iya samun manhajar ta Alipay ko Wechat

Lauyan kamfanin fasaha na Hong Kong da ke aiki a kamfanin DLA Piper Carolyn Bigg ta fada wa BBC cewa: "A China da kuma sassan Asia, ana ganin akwai bukatar yin amfani da bayanan da ake samu a maimakon dauke kai daga kansu matukar an yi cikin gaskiya tare da neman izini a wajen da ake bukatar hakan."

'Daga bangaren China, manhajar tana da mahimmanci ga jama'a... Hakan ya nuna amfanin bayanai musamman idan aka yi amfani da su yadda ya kamata," a cewarta.

Gwamnatin China ta bayyana irin "kusancin" a matsayin kusantar wanda ake zargi ko kuma aka tabbatar ya kamu da coronavirus ba tare da wata kariya ba lokacin da mutumin yake rashin lafiya ko da kuwa basu nuna alamu a lokacin ba.

Kusancin ya hada da:

  • Mutanen da suke aiki tare, suke zama a aji daya ko kuma suke zaune a daki daya
  • Ma'aikatan lafiya da iyalai ko sauran mutane da suke mua'amala da mara lafiya da masu kula da su
  • Fasinjoji da matuka jirgin sama ko jirgin kasa ko sauran hanyoyin sufuri da suka kasance tare da mai dauke da cutar

Misali, duk fasinjojin jirgin sama da suka zauna tsakanin layuka uku da mutumin da ya kamu da cutar, da kuma ma'aikatan jirgin, ana ganin sun samu kusanci sosai yayin da sauran fasinjojin kuma za a iya cewa sun kusanci mutumin.

Dangane da jiragen kasa masu na'urar sanyaya daki da fasinjoji da ma'aikatan jirgin suma ana ganin sun samu kusanci da mai cutar.