'An kama wadanda suka kai wa Sarkin Potiskum hari'

Shugaban 'yan sandan Najeriya

Asalin hoton, @PoliceNG

Lokacin karatu: Minti 1

'Yan sanda a Najeriya sun ce sun kama wadanda ake zargi da kai wa Sarkin Potiskum, Alhaji Umaru Bubaram, hari a kan babban hanyar Kaduna zuwa Kano ranar Talata 14 ga watan Janairun 2020.

Maharan sun bude wa ayarin motocin sarkin wuta, abin da ya yi ajalin mutum shida - biyu fasinjoji da ke tafiya a hanyar, hudu kuma daga cikin jama'ar sarkin - a cewar DSP Yakubu na runduynar 'yan sanda ta jihar Kaduna.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Rundunar 'yan sandan kasar ta ce mutum ukun da take tsare da su sun tabbatar da hannunsu a harin da aka kai wa basaraken.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Sanarwar da rundunar ta fitar a shafinta na Twitter ta ce mutanen na da hannu a ayyukan ta'addanci da garkuwa da mutane a sassan arewacin kasar kuma suna bai wa 'yan sanda muhimman bayanai.

Kakakin 'yan sandan kasar Frank Mba ya ce rundunar na bincike domin dakile aiyukan kungiyar da sauran bata gari.

Da yake kira ga jama'a da su nuna kishin kasa ta hanyar bayar da bayanai kan bata gari, Frank Mba ya koka bisa yadda wasu 'yan kasar ke rufa wa miyagu asiri.