An harbe sojan da ya kashe mutum 26 a Thailand

Asalin hoton, EPA
An kashe wani soja bayan ya harbe mutum 26 cikinsu har da kwamandan rundunar da yake aiki a karkashinta.
Jami'an tsaron Thailand sun bindige sojan ne bayan shafe sa'a 12 ana musayar wuta tsakaninsu da shi a wata cibiyar kasauwanci.
Maharin ya jikkata mutum 57 bayan wadanda ya harbe da makaman da ya kwasa a wani sansanin soji bayan ya kashe kwamandan rundunar da wasu mutum biyu.
Da misalin karfe 2 na ranar Asabar ne mazauna Nakhon Ratchasima suka fara jin karar harbi, inda jami'an tsaro suka yi ta kokarin kubutar da mutane daga cibiyar kasuwancin da kuma dakile maharin.
Ministan lafiya Anutin Charnvirakul, ya jinjina wa 'yan sanda da sojoji bisa yadda suka yi wa dan bindigar kofar rago har suka kawo karshen harin.
Yayin dubiyar wadanda suka samu raunuka, Firai Minista Prayuth Chan-ocha ya ce ba a taba samun mummunan lamari irinsa ba a kasar.
Ya kara da cewar sojan ya dauki makami ne saboda zargin an damfare shi a cinikin gidansa da aka yi.
Yayin dauki ba dadin, sojan ya rika wallafa hotunan makaman da ke hannunsa tare da tambaya ta shafinsa na Facebook, ko shin ya mika wuya?











