Wani soja ya bude wa mutane wuta a Thailand

Asalin hoton, Facebook
Wani soja ya bude wa abokan aikinsa wuta tare da kashe mutum 12 a yankin arewa maso gabashin Birnin Bangkok na kasar Thailand.
Kafafen yada labaran kasar sun ce an yi ta dauki ba dadi da kokarin cin karfin maharin.
Ma'aikatar tsaron kasar ta ce sojan, Jakraphanth Thomma, ya kai wa kwamandansa hari sannan ya dauki bindiga da harsasai a wani sansanin soji.
Kakakin rundunar tsaron kasar ya ce sojan ya wuraren da jami'in sojin bude wa wuta sun hada da wani sansanin soji da wani babban shago da kuma wurin ibadar mabiya addinin Buddha.
Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta ce maharin na boye a ginin karkashin kasa na cibiyar kasuwancin.
Hukumomin kasar na rufe kofofi da sauran sassan ginin a kokarinsu na hana maharin tserewa.







