Shugaban da zai karbi albashin naira miliyan 36 a rana guda

Asalin hoton, EPA
Wani shugaban lardi a Jamus wanda aka cire daga kan mukaminsa zai karbi albashi da alawus da suka kai euro 93,000, wato kusan naira miliyan 37 saboda aikin kwana daya da ya yi.
Jam'iyyar AfD ce ta goyi bayansa lokacin da yake neman mulki.
Jaridar The RND (Editor Network Germany) ta ce hukumomin Thuringia sun tabbatar mata cewa albashin da za a bai wa Kemmerich gaskiya ne.
Dan siyasar Liberal FDP mai sassaucin ra'ayi, Thomas Kemmerich, ya ajiye aikinsa ranar Alhamis, kwana guda bayan 'yan majalisar Thuringia sun amince da shi a zaben da ya bai wa kowa mamaki wanda jam'iyyar AfD ta mara masa baya.
Zaben ya fusata 'yan siyasar Jamus da dama.
Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana zaben a matsayin wani abu da "ba za a yafe ba" tana mai cewa dole a sauya sakamakonsa.
Har yanzu dai ba a zabi mutumin da zai maye gurbin Mr Kemmerich ba. Amma ana kiraye-kiraye a gudanar da sabon zaben lardi a Thuringia, ko da yake jam'iyyar Shugaba Merkel ta Christian Democrats (CDU) ta yi watsi da kiraye-kirayen.
A karshen mako ne kuma CDU da jam'iyyar Social Democrats (SPD), za su yi wata tattaunawa game da batun.











