Trump ya sallami wadanda suka bayar da shaida a kansa

Asalin hoton, AFP
Shugaba Amurka Donald Trump ya sallami manyan jami'ai gwamnatin guda biyu da suka bayar da shaida a kansa a lokacin da majalisar kasar ke sauraren karar tsige shi.
Jakaden Amurka a Tarayyar Turai, Gordon Sondland ya fitar da sanarwa cewa an gaya masa an cire shi daga mukaminsa.
Wakilin BBC ya ce "Gordon Sondland ya shaida wa masu bincike cewa akwai yiwuwar hana Ukraine agaji da Mista Trump ya yi na da alaka da siyasa.
Shugaba Trump ya musanta zargin kuma majalisar dattawan kasar ta wanke shi daga zargin amma kuma sai ga shi ya koro Sondland daga mukaminsa nan take."
A baya dama lauyan wani jami'in Majalisar Tsaron Amurka wanda ya bayar da shaida a sauraren karar ya ce an kori wanda ya ke wakilta, Laftanal Kanal Alexander Vindman daga aikinsa a fadar White House.
Lauyan ya ce an kori Kanal Vindman ne saboda ya fadi gaskiya.
A lokacin sauraren karar, Kanal Vindman, wanda kwararre ne a kan harkokin Ukraine- ya ce ya taba jiyo Mista Trump da Shugaban Ukraine suna magana a waya kan wani batu da bai dace ba.
A baya Shugaba Trump ya shaida wa manema labarai cewa ransa a bace yake a kan hafsan sojin.










