Yadda gwamna ke kallon rikicin Boko Haram a Yobe

soja

Asalin hoton, Getty Images

Yawaitar hare-haren kungiyar Boko Haram da ISWAP a arewa maso gabashin Najeriya a baya-bayan nan na kara haddasa asarar rayukan farar hula da jami'an tsaro, abin da ya sa ake ganin babban titin Maiduguri zuwa Damaturu tamkar tarkon mutuwa.

Matsalar tsaron ta sa mutane da dama a Najeriya na neman shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sauya manyan hafsoshin tsaron kasar ya nada sabbin jini su gwada tasu dabarar.

Jihar Yobe daya ce daga cikin jihohin da matsalar ta fi kamari, kuma a yayin wata ziyara a ofishinmu na Landan, gwamnan jihar Mai Mala Buni, ya bayyana wa Shugaban Sashen Hausa na BBC, Aliyu Abdullahi Tanko, yadda ya ke kallon lamarin na masu tayar da kayar baya.

"Mu ne zahirin wadanda abin ya addabe mu kuma mu muka san me muke ciki kafin shekarar 2015,'' in ji gwamnan.

"Yana da wuya a fahimci irin saukin da aka samu ba tare waiwayar halin da jihar ke ciki a baya ba,'' a cewarsa.

Gwamnan ya kara da cewa a shekarar 2013, kungiyar Boko Haram ta kwace ikon yawancin garin Damaturu, har tana zartar da hukuncin shari'a a kan mutane da dukan matan da suka fito babu hijabi.

Wasu mazauna jihar na ganin ana neman komawa gidan jiya duk da yadda gwamnati ke cewe an samu nasarori da saukin hare-haren kungiyoyin tayar da kayar bayan.

Mutanen na cewa har yanzu ba sa iya yin barci da idanunsu a rufe a halin yanzu, kamar yadda Aliyu ya kara tambayar gwamnan.

Gwamnan ya ce duk da haka matsalar ta yi sauki, amma wanda bai san halin da jihar ke ciki a baya ba, da irin abin da ke faruwa a tsakanin hanyar Damaturu zuwa maiduguri ba, da wuya ya fahimci saukin da aka samu a yanzu.

Wannan layi ne

''Shi yasa Allah ke cewa idan muka gode maSa sai ya kara mana. Mu muna gode wa Allah, saboda saukin da aka samu.

"A cikin jihar Yobe, kananan hukumomi guda biyu, Gulani da Gujba a hannun Boko Haram suke."

Ya ce "Bar ma maganan kauyukansu, hatta hedikwatar kananan hukumomin da ma sakatariyarsu Boko Haram ne ke ciki. Yau ba sa ciki.''

Amma yanzu babu wata karamar hukuma a jihar da ke hannun ikon Boko Haram," kamar yadda ya shaida wa Aliyu.

Manyan hafsoshin tsaro

Wasu 'yan kasar na neman shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sauya manyan hafsoshin tsaron kasar saboda rashin gamsuwa da kamun ludayinsu, gwamnan ya bayyana godiya ga Allah game da saukin da ya ce an samu.

"Ni na san a da yanzu, shingaye na bincike idan ka tashi daga Damaturu za ka je Maiduguri, ba za ka iya kirgawa ba.

"In ka tashi daga Damaturu za ka Kano Allah kadai Ya san shingaye na jami'a tsaro da za ka wuce. Sannan idan ka tashi daga Kano za ka Abuja, shingaye nawa ne na jami'an tsaro?" ya kare da tambaya.

Wannan layi ne

Hayar Damaturu zuwa Kano?

BBC ta kuma tambaye shi halin da hanyar Maiduguri Damaturu zuwa Kano take ciki a yanzu.

Gwamnan ya bayyana cewa a baya-bayan nan an samu matsala amma an samu raguwar matsalar a cikin makon nan da ake ciki.

"Jami'an tsaro suna iya kokarinsu. Sannan hadin kan da suke samu daga mazauna yankin da gwamnatocin jihohin yankin da suka hada da Borno da Yobe, na taimaka wa kwalliya na biyan kudin sabulu."

Karin sojoji

Ya ce maganar da ake yi ta kara yawan jami'an tsaro da kayan yaki a yankin abu ne da ya kamata.

Shin gwamnan na ganin jami'an tsaron za su iya yin wannan yakin?

Da yake amsa tambaya a matsayin babban jami'in tsaron jihar game da gamsuwarsa bisa yadda jami'an tsaron ke gudanar da aiki a yankin, Mai Mala Buni ya ce sojojin na kokartawa.

"Suna iya kokarinsu. Da ni da dan uwana da sauran al'umma muna kwance a gidajenmu, su ba sa barci. Sau nawa ake yunkurin shiga garuruwa? Jami'an tsaon ne ke hanawa.

"Duk abin da ake yi din nan fa sai dai a dauki matakai na yadda za a inganta. Ya kamata a gane cewar shin sojoijn nan ma suna da kayan yaki?

Wannan layi ne