India: An kama mutumin da ya yi wa 'yar shekara 5 fyade a ofishin jakadancin Amurka

Representational image: protest against sexual violence against women in India.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An sha yin zanga-zanga a Indiya kan yi wa mata fyade

An kama wani mutum mai shekara 24 bisa zargin sa da yi wa yarinya 'yar shekara biyar fyade a harabar ofishin jakadancin Amurka da ke Delhi, babban birnin kasar Indiya.

An kama mutumin ne ranar Lahadi bayan da iyayen yarinyar suka shigar da korafi ga hukuma, kamar yadda 'yan sanda suka sanar da kamfanin dillancin labarai na PTI.

Yarinyar, wacce aka ci wa zarafi ranar Asabar da safe tana samun sauki. Amma likitoci sun tabbatar da cewa an yi mata fyade.

Iyayenta suna zaune ne a cikin ofishin jakadancin, inda mahaifinta ke aiki a matsayin daya daga cikin masu kula da wajen.

'Yan sanda sun ce mutumin da ya yi mata fyaden wani direba ne, sai dai ba ofishin jakadancin ne ya dauke shi aiki ba.

Amma yana zaune ne da iyayensa a gidajen ma'aikata na ofishin inda babansa ke aiki.

Ofishin jakadancin Amurkar na Chanakyapuri, wani yanki da ke tsakiyar birnin Delhi inda mafi yawan ofisoshin jakadancin kasashen waje a can suke.

Ofishin babba ne da ya kai girman eka 28 kuma yana cike da tsananin tsaro.

Akwai sanayya tsakanin iyalan wanda ake zargin da na yarinyar sosai, a cewar masu bincike, wadanda suka shaida wa jaridar Hindustan Times cewa ya yaudari yarinyar ne zuwa gidansa a lokacin da ya ganta tana wasa a waje.

Iyayensa ba sa gida a lokacin da abin ya faru.

A yayin da yarinyar ta koma gida, ta shaida wa mahaifiyarta abin da ya faru. Nan da nan aka kai ta asibiti, inda 'yan sanda suka ce, likitoci sun tabbatar da cewa an mata fyade.

'Yan sanda sun ce ana binciken mutumin a karkashin dokokin Indiya da ke bai wa yara kariya.

A shekarar 2018 ne gwamnatin Indiya ta gabatar da hukuncin kisa ga duk wanda ya yi wa yara fyade, kan wasu abubuwa biyu da suka faru na yi wa 'yar shekara takwas da 'yar shekara 16 fyade.

A cewar kididdigar baya-bayan nan ta Indiya kan aikata miyagun laifuka, cikin duk mutum hudun da ake wa fyade to akwai yarinya daya - kuma kashi 94 cikin 100 na wadanda ake yi wa din sun san masu aikata hakan.